Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa a Nijeriya NEMA, ta ce mutum 259 ne suka mutu yayin da wasu 625,239 suka rasa matsugunansu sakamakon iftila'in ambaliyar ruwa a Nijeriya a tsakanin watan Afrilu zuwa Satumban 2024.
Kazalika hukumar ta ce mutane 1,048,312 ne iftila'in ya shafa a jihohi 29 da ƙananan hukumomi 172 a faɗin ƙasar, kamar yadda Darakta-Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar ta bayyana a cikin rahoton taron gaggawa na ƙasa (ECF) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Shugabar ta jajanta wa waɗanda lamarin iftila'in ya shafa tare da su tabbacin cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya karkashin hukumar NEMA za ta ba da dukkan tallafin da ya kamata kana ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan da suka dace.
A cewarta, makasuɗin kiran taron, shi ne don a samu bayanai kan lamarin ambaliyar a ƙasar tare da bai wa masu ruwa da tsaki ayyukan da za su taka rawa akai.
Ta ce ana kan ƙoƙarin ganin an rage tasirinsa wahalhalun da yanayin ya haifar, duk kuwa da cewa ba za a iya daƙile aukuwar iftila'in ambaliyar gaba ɗaya ba.
''NEMA ta samar wa mutanen da suka rasa matsugunansu sansanoni a wasu jihohi tare da tura ƙarin ma'aikata don taimakawa a ayyukan bincike da ceto.
Haka kuma, hukumar ta samar da kayan aiki na tsaftace ruwa da aikin bincike da ceto ga jihohin da lamarin ya shafa,'' in ji ta.
Ta kuma ya zuwa yanzu dai lamarin bai fi ƙarfin gwamnatin Nijeriya ba.
A mummunan iftila'in da ya afka wa jihar Borno kuwa sakamakon fashewar Madatsar Ruwa ta Alau, NEMA ta ce an fara samun janyewar ruwan a birnin Maiduguri, sannan al'amura na yau da kullum sun soma komawa daidai a babban birnin.
"Ba za mu ce mun kawo ƙarshen aikinmu ba, za mu ci gaba da ba da agajin gaggawa ba dare ba rana tare da sa ido da kuma tantance yanayin da ake ciki, don haka yana da muhimmanci ci gaba da bayyana yanayin da ake ciki.