Akalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani wurin hakar ma'adinai a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya . Hoto: Caleb Muftwang/X

Akalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani wurin hakar ma'adinai a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Wani jami’in gwamnati a jihar, Joshua Riti, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu na Turkiyya a ranar Talata cewa wadanda abin ya shafa ‘yan shekaru tsakanin 18 zuwa 30 ne kuma ‘yan karamar hukumar Bassa ne.

Ya kara da cewa, rugujewar ta afku ne a ranar Asabar a kan iyakokin kananan hukumomin Bassa, Jos ta Kudu, da Jos ta Arewa, inda wadannan matasa suke neman abin dogaro da kai a cikin ramin hakar ma’adinai.

A baya-bayan nan masu hakar ma’adinai 22 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani ramin hakar ma’adinai a wani haramtaccen wuri da ke cikin wani wurin gandun namun daji da ke yankin karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba da kuma karamar hukumar Toungo a jihar Adamawa.

AA