Ana fargabar adadin mutanen da suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale ɗauke da mata da yara a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Neja a Nijeriya ya haura mutum 100, a cewar ma'aikatan ceto a yayin da suka ciro ƙarin gawawwaki daga Kogin Neja.
Kimanin fasinjoji 300 da ke kwale-kwalen na kan hanyarsu ta zuwa taron maulidi a lokacin da kwale-kwalen nasu ya kife, in ji jami'an yankin.
An ciro gawawwakin mutane 36, an kuɓutar da wasu 150, in ji wani mai magana da yawun gwamnati, Ibrahim Audu Husseini yayin zantawa da kamfanin dillanacin labarai na AFP.
"Mun gano gawawwaki 20 yau. Wannan ya kawo adadin gawawwakin da aka gano daga kogin zuwa 36."
Babu "yiwuwar" za a samu wasu da rai, in ji shi. "Babu yadda za a yi a ce akwai wani da yake da rai tsawon kwanaki uku a ƙarƙashin ruwa. Aikin da ake yi yanzu shi ne a tsamo gawawwakin da suka ɓace."
Mahukuntan ba su bayyana musabbabin kifewar kwale-kwalen a Gbajibo da ke kusa da Mokwa ba, amma sun ce ya kife da misalin ƙarfe 8:30 na dare.
Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da bincike
A wata sanarwa da aka fitar a yammacin Alhamis, shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaicinsa kan aukuwar lamarin, kuma ya yi kira da a gudanar da bincike kan haɗurran kwale-kwale a baya-bayan nan a ƙasar.
Fadar shugaban ƙasar ta ce "Shugaban Ƙasa Tinubu na jajanta wa iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su kuma yana addu'ar samun jinƙai ga waɗanda suka mutu."
Shugaban ya bayar da umarni a hukunta duk masu tuƙa kwale-kwale da daddare ba tare da kariya ba wanda hakan ya saɓa wa dokokin ƙasar.
Tinubu ya kuma gode wa ma'aikatan agajin gaggawa inda ya kuma yaba wa masu ninƙaya don neman mutane a cikin ruwan.
Kifewar kwale-kwale a Nijeriya
Ana yawan samun kifewar kwale-kwale a kogunan Nijeriya da ba su da dokokin amfani da su, musamman a lokutan damina idan kogunan suka batse.
Loda mutane ya wuce ƙa'ida da rashin kula da lafiyar kwale-kwale ne ke haddasa kifewar su.
A baya mahukuntan kogunan Nijeriya sun yi yunƙurin hana hawa jiragen ruwa da kwale-kwale da daddare, kuma suka ce lodin mutane da kayan da ya wuce ƙima babban laifi ne, amma masu kwale-kwalen suna karya waɗannan dokoki.
A watan jiya, wani kwale-kwale da aka yi wa lodin a ya wuce ƙima ya kife ɗauke da manoma sama da 50 a Kogin Gummi da ke jihar Zamfara. A bayyana mutuwar sama da mutum 40.
A watan Yunin 2023, fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani kwale-kwale ɗauke da kimanin mutane 250 ya kife a jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, ɗaya daga cikin haɗurran kwale-kwale da aka fi rasa rayuka a 'yan shekarun nan.