Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Libya sun zarta 2000

Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Libya sun zarta 2000

Hotuna daga wurin da ambaliyar ruwan ta faru sun nuna yadda ruwa ya shanye gine-gine.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki. Hoto/AA

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Derna na kasar Libya ya zarta 2,000, a cewar kafafen watsa labaran kasar ranar Litinin.

An yi amannar dubban mutane sun bata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Libyan News Agency (LANA) ya ambato Ossama Hamad, shugaban majalisar dokokin da gwamnati ta nada, yana cewa.

Hamad ya ce ambaliyar ruwan ta shafe dukkan rukunin gidajen Derna.

Wasu bidiyoyi da mazauna yankin da bala’in ya fadawa suka dauka sun nuna yadda gidaje suka rushe da kuma yadda ruwan ya shafe su.

Tun da farko a ranar ta Litinin, shugaban gwamnatin hadin kan kasa, Abdul Hamid Dbeibeh, ya bayyana dukkan yankunan da ke fuskantar ambaliyar ruwa a matsayin “yankuna masu hatsari.”

Dbeibeh ya sanar da makokin kwana uku na kasa baki daya sakamakon wannan bala'i.

Rahotannin farko sun ce mutum “akalla mutum 15 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa biyo bayan ruwan sama wanda guguwar Daniel ta jawo a Derna,” kamar yadda mai magana da yawun hukumar gudanarwa ta Benghazi da ke Libiya ya shaida wa AFP.

Ya bayyana cewa firaiministan gwamnatin gabashin kasar, Oussama Hamad da shugaban kwamitin ceto da sauran ministoci sun tafi Derna domin ganin irin barnar da ambaliyar ta yi.

Kwararru sun bayyana wannan guguwar ta Daniel a matsayin mai tsanani.

Guguwar ta faru a gabashin Libiya a ranar Lahadi da rana, inda ta fi illa a birnin Benghazi da har aka saka dokar hana fita haka kuma aka rufe makarantu tsawon kwanaki.

TRT Afrika