Aƙalla mutane 19 ne suka mutu sakamakon tashin wani bam a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Mazauna yankin dai na zargin mayaƙan Boko Haram ne suka dasa bam ɗin da ya tashi ranar Laraba da daadare.
''Bam ɗin ya tashi ne ranar Laraba da misalin karfe 8:05 na dare a wani wurin sayar da shayi inda 'yan garin suke zama don hira,'' kamar yadda wani jami’in gwamnati a ƙauyen Kawuri wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa maneman labarai, yana mai ƙarawa da cewa mutane da dama sun jikkata.
“Babu wanda zai iya bayyana takamaiman yadda lamarin ya faru, amma muna zargin dasa bam ɗin aka yi, ba harin ƙunar bakin wake ba ne,'' in ji shi.
Jami'in ya kuma bayyana cewa “Mun ga gawawwakin mutane 19 da fararen-hula da dama ba a tantance adadinsu ba waɗanda suka jikkata.''
''An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti a Maiduguri domin ba su kulawa,”in ji shi.
Kazalika lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu 'yan ta'addan sun kai ''hari Ofisin 'yan sanda a garin Jakana da ke ƙaramar hukumar Konduga, inda aka kashe wani ɗan sanda da wata mata tare da ƙona wasu motocin sintiri guda biyu a wurin,'' kamar yadda jaridun ƙasar suka rawaito.
Ƙauyen Kawuri dai na da nisan kilomita 50 daga cikin Maiduguri, kan hanyar Konduga da Bama.
Kawo yanzu dai hukumomi a jihar ta Borno ba su fitar da wata sanarwa ko ƙarin bayani dangane da lamarin ba.
Jihar Borno ta kwashe shekaru da dama tana fama da hare-haren 'yan Boko Haram waɗanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.