Mutane da dama sun ɓata a Ethiopia bayan kwale-kwale ya kife a wani tafki mai cike da kadoji

Mutane da dama sun ɓata a Ethiopia bayan kwale-kwale ya kife a wani tafki mai cike da kadoji

Wani kwamandan ‘yan sanda na yanki ya ce mutanen 15 waɗanda aikinsu shi ne sauke ayaba su ne a cikin kwale-kwalen.
An yi wa kwale-kwalen lodin ayaba lokacin da lamarin ya faru. / Hoto: Reuters

Mutane goma sha huɗu sun ɓace bayan wani kwale-kwale ya kife a wani tafki a kudancin Ethiopia, a cewar ‘yan sanda.

Kwale-kwalen, wanda aka loda masa ayaba, ya nutse ne ranar Alhamis a tafkin Chamo, kudu da babbban birnin ƙasar Addis Ababa, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya bayyana ranar Juma’a.

Tafkin na Chamo, wanda ke zurfin ƙafa 14, matattarar kadoji da dorinar ruwa ne.

Masu ceto sun gano mutum biyu da ba su nutse ba, saboda sun riƙe jarka ta mai, a cewar hukumomi, inda suka ƙara da cewa ana ci gaba da bincike don gano wasu fasinjojin.

Mutanen 15 waɗanda aikinsu shi ne sauke ayaba su ne a cikin jirgin a cewar kwamandan ‘yan sandan yankin Reta Tekla. Har yanzu ba a san abin da ya sa kwale-kwalen ya kife ba.

AFP