Mun daƙile yunƙurin 'yan kirifto na tallafa wa masu zanga-zanga da N83bn: Ribadu

Mun daƙile yunƙurin 'yan kirifto na tallafa wa masu zanga-zanga da N83bn: Ribadu

Kudaden sun haɗa da gudunmawar wasu manyan 'yan siyasa a Abuja, Kaduna, Kano da Katsina, in ji Malam Nuhu Ribadu.
A ranar 1 ga Agustan 2024 ne 'yan Nijeriya suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da mumunan jagoranci da tsadar rayuwa a fadin kasar : TRT Afirka

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta gano kuma ta daƙile wani yunƙuri na tura kuɗi kimanin Naira biliyan 83 ga mutanen da suka shirya zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar.

Mai bai wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan a wajen taron Majalisar Ƙoli ta Kasa da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

A jawabin da ya gabatar mai taken 'Zanga-Zanga a Faɗin Nijeriya Da Yadda Ta Shafi Tsaron Ƙasa', Ribadu ya ce kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan 50 na kuɗin kirifto, da Naira biliyan huɗu da wasu 'yan siyasa suka bayar a Abuja, Kaduna, Kano da Katsina.

Mashawarcin shugaban Nijeriya kan sha'anin tsaro ya ce sun kuma gano wani Bature a matsayin mai ɗaukar nauyin ɗaga tutocin ƙasashen waje a lokacin zanga-zangar.

Wata majiya ta bayyana cewa "Mai Bai wa Shugaban Ƙasar Shawara ya ce gwamnati ta yi nasarar ganowa da daƙile yunƙurin aika dala miliyan 50 zuwa asusun kirifto da za a yi amfani da shi a lokaci zanga-zanga. Sun toshe asusu huɗu da ke ɗauke da dala miliyan 38."

"Kazalika sun gano wasu manyan 'yan siyasa da suka bayar da gudunmawar naira biliyan huɗu don ɗaukar nauyin zanga-zangar," in ji majiyar.

Akwai masu daukar nauyin zanga-zangar a ciki da wajen Nijeriya

An rawaito Ribadu na cewa akwai wannun wasu 'yan ƙasashen waje a cikin zanga-zangar, sun gano wasu 'yan ƙasashen waje ne suka rura wutar zanga-zanga a Nijeriya.

“An samu wani ɗan ƙasar waje da hannu dumu-dumu wajen ɗaukar nauyin zanga-zangar, wanda a makon nan 'yan sanda za su bayyana suna neman sa ruwa-a-jallo."

Ya ce ana ci gaba da neman wannan mutum amma kuma an kama wadanda yake hada baki da su a cikin kasar a yankunan Abuja, Kaduna da Kano.

A ranar 1 ga Agustan 2024 ne 'yan Nijeriya suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da mumunan jagoranci da tsadar rayuwa a fadin kasar.

Zanga-Zangar ta rikiɗe zuwa rikici da fasha shaguna a wasu jihohin arewacin Nijeriya inda mutane sama da 20 suka rasa rayukansu. An kuma yi ɓarnatar da dukiyoyin gwamnati da na jama'a a yayin zanga-zangar.

TRT Afrika