Kawo yanzu gwamnati ba ta bayyana adadin wadanda suka mutu a hatsarin ba. Hoto/Facebook: Governor Simon Lalong

Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Jos na Jihar Filato a arewacin Nijeriya.

Jami'in 'yan sandan da ke kula da shiyyar A ta birnin, Obinna ya tabbatar wa TRT Afrika afkuwar lamarin, sai dai ya ce zuwa yanzu ba a san yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Hatsarin ya faru ne a ranar Alhamis da da misalin karef 1.30 na rana a kan titin zuwa Bauchi sakamakon faduwar wata babbar motar dakon man fetur.

Ganau da yawa sun shaida wa TRT Afrika cewa faduwar motar ke da wuya sai ta kama da wuta kuma nan take wutar ta gawurta inda ta laso wasu motocin da ke tafiya akan titin da ma wadanda suke ajiye a gefen titi.

"Muna kyautata zaton birki ne ya tsinke wa mai motar," kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya fada wa TRT Afrika.

Zuwa yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata ba, amma wasu rahotanni sun ce fiye da mutum 10 ne suka rasa rayukansu.

A wasu bidiyo da TRT Afrika ta gani, ta ga yadda wajen ya turnuke da hayaki da motoci da ke cin wuta da kuma wata gawa da aka dauko a wulbaro ta kone kurmus.

Rundunar 'yan sandan ba ta yi wa TRT Afrika karin bayani ba, amma Mista Obinna ya ce nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa kan sakamakon binciken da suka yi na yadda lamarin ya faru.

TRT Afrika da abokan hulda