An buɗe taron kwana biyu na majalisar zartarwar ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 45 a Accra babban birnin Ghana a ranar Alhamis.
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Afirka da wakilan ƙasashen za su tattauna tare da amincewa da kasafin kuɗin AU mai wakilai 55 na shekarar 2025 da sauran batutuwan da suka shafi nahiyar.
Ana kuma sa ran taron na zai yi bayar da shawarwari kan rawar da ƙungiyar AU za ta taka a taron shugabannin ƙasashen G20 da za a yi a watan Nuwamba a Brazil.
Ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola ne zai jagoranci tawagar ƙasarsa a taron, in ji wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Turkiyya Anadolu ya rawaito.
Taron zai yi nazari tare da amincewa da kasafin ƙudin ƙungiyar ta AU na shekarar 2025 wanda ke da muhimmanci wajen ciyar da ayyukanta gaba.
Ƙungiyar dai ta ƙuduri aniyar aiwatar da manufofinta na 2063 da kuma sauran manyan ayyukanta ciki har da batun daƙile shirin sayar da bindigogi.
Kazalika sanarwar ta ce, jagorancin Mista Lamola ya nuna muhimmancin ƙarfafa ƙungiyar da sassanta tare da samun ‘yancin kanta da ke zama wani muhimmin mataki na tunkarar ƙalubalen ci gaba da nahiyar ke fuskanta.
Akwai dai yiwuwar manyan jami'an diflomasiyya da sauran ministocin ƙasashen Afirka mambobin AU su taɓo batutuwan da suka shafi rashin tsaro da nahiyar ke fuskanta, kamar na ƙungiyoyi masu ta da ƙayar baya a Yammacin Afirka da yankin Sahel, da kuma ƙasar Somaliya da rikicin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC).
Haka kuma Afirka na fama da ƙalubale na sauyin yanayi, wanda tasirinsa ya shafi yanayin samar da abinci da ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane.
A yayin taron, Lamola zai kuma tattauna da takwarorinsu na sauran ƙasashen Afirka, in ji sanarwar daga ofishinsa.