Daga Shamsiyya Hamza Ibrahim
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta dukufa wajen lalubo hanyoyin bunkasa fannin samar da isasshe abincin dabbobi mai dauke da sinadaran gina jiki, da ma sauran albarkatun noma.
A baya-bayan nan Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta kasar tare da hadin gwiwar abokan huldarta sun bullo da wani tsari da za a bi wajen samar da albakatun abincin dabbobi a kasar.
Sun dauki matakin ne a wurin taro na kwana biyu da ma’aikatar ta gunadar a Abuja wanda aka kammala ranar Alhamis.
Taron, wanda shi ne karo na biyu, an yi masa take da "samar da karin hanyoyin albarkatun abincin dabbobi masu dorewa."
Ya samu halartar kwararru kan fannin kiwo da manoma da na gwamnati da kamfanonin sarrafa abincin dabbobi da manyan 'yan jarida da kuma malamai a fannin ilimin noma da sauran masu ruwa da tsaki.
Kazalika taron ya duba matakin rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin daidaituwar farashi a masana’antar samar da abincin daddobi a Nijeriya.
'Kokarin cika manufofin gwamnati'
Ministan Ayyukan Noma da Raya Karkara a Nijeriya Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, ya shaida wa TRT Afrika cewa taron na daga cikin manufofi da burin da gwamnatin kasa ke da shi don inganta tsarin samar da abincin dabbobi wadatacce, da samar da tsaro da kuma hanyoyin adana abincin.
"Gudunmawar abincin dabbobi a fannin Noma a Nijeriya na da matukar muhimmanci domin zai samar da muhimman sinadaran gina jiki da za su taimaka wa dabbobi da kuma ayyukan noma," a cewar Dr. Abubakar.
Ya kara da cewa "akwai karancin abincin dabbobi a Nijeriya, kuma kasar na da albarkatu da yanayin ayyukan noma da dama amma akasarin manoma ba su da masaniya a kan hakan, shi ya sa ake samun wadannan matsaloli."
"Manoma sun ki sauya wa daga tsofaffin hanyoyin da aka saba yi a baya duk da cewa a halin da ake ciki duniya ta ci gaba’’ in ji ministan.
Kalubalen samar da isasshen abincin dabbobi
Kasancewar Nijeriya na da yawan al’umma sama da mutum miliyan 200, adadin da ake hasashen zai iya karuwa, akwai bukatar samar da isasshen abinci da ke da sinadaran gina jiki ga dabbobi.
Kuma yana da kyau manoma su kara kaimi daga bangarensu wajen anfani da ci gaban da zamani ya zo da su don wadatar da bukatun al’ummar kasa, a cewar Dakta Mahmood.
A hirar da TRT Afirka ta yi da wani kwararre a fannin harkokin noma a Nijeriya, Prince Ade Ajayi, ya ce rashin noman hatsi wadatacce da zai samar da abincin dabbobi na daga cikin kalubalen da makiyaya ke fuskanta.
"Misali kowane dan adam da dabba na bukatar tsirrai don ya rayu, don haka idan babu tsirrai da saiwa da masu kiwo za su bai wa dabbobinsu, ba wani zabin da suke da shi da ya wuce su dogara ga shukokin da manoma suka yi."
‘’Haka kuma rashin wadatattun sinadaran da za a a yi amfani da su wajen hada abincin dabbobin na zama babban kalubale.
"Mafi yawancin sinadaran daga kasashen irin na yankin Asiya da Turai da kuma Amurka ake shigowa da su don haka dole farashin ya shafi yawan abin da manoma a kasar za su bayar,’’ in ji Mista Ade.
Abin yabawa ne
Makiyaya da dama sun bayyana ra’ayoyinsu game da wannan taro.
Abubakar Bappayo na daga cikin makiyayan da suka halarci taron, ya kuma ce ya kamata a yaba wa gwamnati kan wannan yunkuri.
"Irin mu daga Jihar Bauchi muna fama da matsalolin rashin abinci na dabbobinmu, don ko a bara sai da muka yi asarar dabbobi da dama, kuma hakan ne ya sa muke bulagaro zuwa wasu jihohi da ke makwabtaka da mu irin Filato da Binuwai da Neja saboda can akwai ruwa da abinci.’’
Shi ko Musa Haliru, wani makiyayi da TRT Afrika ta ji ra’ayinsa, ya ce ‘’Hakan ba karamin taimako zai yi ba wajen rage yawan rikice-rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma a Nijeriya.’’
A karshe Minista Abubakar Mahmood ya kara da cewa akwai kyakkyawan hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kungiyoyin da suke harkar noma na cikin gida da na waje da kuma 'yan kasuwa wadanda ke neman hanyoyin fitar da kayansu waje.
"Nijeriya za ta kirkiro da wasu hanyoyi musamman na amfani da kimiyyar zamani kamar yadda sauran kasashen da suka ci gaba ke yi," in ji shi.