Atiku ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.  / Hoto: Reuters

Dan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya ce muddin yana numfashi ba zai daina fafutukar dabbaka dimokuradiyya a ƙasar ba.

Atiku, wanda ya bayyana haka ranar Litinin a taron manema labaran da ya gudanar a Abuja, babban birnin kasar game da halin da kasar ke ciki, ya kuma ba da labarin yadda aka taba yunkurin halaka shi a fafutukar da yake yi wajen tabbatar da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.

Atiku ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, sai dai ya garzaya kotu don kalubalantar nasarar Tinubu.

A makon jiya ne Kotun Koli ta kasar ta yi watsi da karar da ya shigar tana mai cewa ba shi da gamsassun hujjojin da za su sa a soke zaben Shugaba Tinubu.

Amma a taron da ya gudanar ranar Litinin, Atiku ya ce ba zai daina fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a kasar ba.

"A gare ni da kuma jam’iyyata wannan babi na fafutukarmu ya zo karshe. Sai dai ba wai na tafi kenan ba.

"Muddin ina numfashi zan ci gaba da fafutuka tare da sauran ‘yan Nijeriya, don karfafa dimokuradiyya da tsarin doka da kuma yin garanbawul ga tsarin siyasa da tattalin arziki da kasarmu ke bukata don cimma ainhin abin da take da damar yi.

"A yanzu matasanmu ne za su jagoranci wannan fafutukar, wadanda sun ma fi mu damar yin hakan.

"A ko da yaushe ina zaben 'yanci maimakon bauta, ko da kuwa wannan zabin ba zai yi mini dadi ba. Lokacin da na shiga siyasa, babban kalubale shi ne a kori sojoji daga mulki yadda za a dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.

Ya kara da cewa: "Daga baya hakan ya zama wani abu da zai zama fafutuka mai tsawo, kuma a matsayina na daya daga cikin shugabannin fafutukar, an taba neman halaka ni.

Kan labarin yunƙurin kashe shi da aka yi, Atiku ya bayyana cewa an kashe 'yan sanda tara da ke "gadin gidana na Kaduna a yunkurin halaka ni. An tilasta mini yin gudun hijira na wata tara," in ji Atiku Abubakar.

Wani labari mai alaƙa

  • Atiku Abubakar yana matukar nuna kiyayya ga Shugaba Tinubu — APC

'Martani kan ƙalubalen da na yi ta fuskanta'

A martanin da na mayar kan ƙalubalen da na yi ta fuskanta, na shigar da ƙararraki a kotuna, waɗanda suka yi nasarar samar da ɗaukar matakai masu cike da tarihi da suka taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu da dokokin shari’a.

A cikin wannan yanayi da ake ciki mai cike da tarihi, da zaɓi mafi sauƙi a gare ni shi ne bai wuce na ja da baya ba, bayan “fashin nasarata da APC da INEC suka yi min.”

“Amma na je kotunan Nijeriya don neman adalci, har kotun Amurka na je don ta taimaka wajen gano abin da hukumomin da alhakin hakan ya rataya a wuyansu a ƙasarmu suka kasa yi, ciki har da bankaɗo takardun shaidar karatun mutumin da aka rantsar a matsayin shugaban ƙasarmu, don a gano ko ainihin wane ne shi.

"Na gabatar da shaidar da na samo da taimakon Kotun Amurka ga Kotun Ƙolinmu don ta yi adalci a kan lamarin.

"Na ba da wannan bayanin ne don a gane cewa abin da a yanzu muke fama da shi ya fi gaban takarar shugaban ƙasa ɗaya ko biyu kuma ya fi Atiku Abubakar.

"Ba batu ne da ya ta’allaƙa a kaina ba; lamari ne da ya shafi ƙasarmu, Nijeriya. Batu ne na irin rayuwar da muke so mu bar wa al’umma mai zuwa da kuma irin misalin da muke so mu bar wa ƴaƴanmu da jikokinsu.

TRT Afrika