Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe duka ofisoshinsa da ke faɗin Nijeriya.
MTN ɗin ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter, amma bai sanar da ranar da zai sake buɗe su ba.
Wannan na zuwa ne bayan wasu fusatattun masu amfani da layin na MTN sun kai hari ga ɗaya daga cikin ofisoshin kamfanin a Legas a ranar Litinin.
A wani bidiyo wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Litinin, an ga wasu fusatattun mutane suna ƙoƙarin kada katangar ƙarfe da ke wajen ofishin na MTN.
Rahotanni sun ce waɗanda suka far wa ofishin na MTN sun aikata haka ne bayan an toshe musu layinsu sakamakon cikas da ke da akwai tsakanin layin nasu na MTN da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN.
MTN ɗin ya ce duk da ya rufe ofisoshin nasa, amma za a iya tuntuɓar ma’aikatansa ta wasu hanyoyin sadarwa.
Haka kuma rufe ofisoshin na MTN na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin soma zanga-zangar da ake tunanin za a yi a Nijeriya a ranar 1 ga watan Agusta.