Aƙalla mutum 71 ne suka rasu a Ethiopia a lokacin da wata babbar mota cike da fasinjoji ta faɗa a cikin kogi, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama da ke kudancin ƙasar ya tabbatar.
Hatsarin wanda ya laƙume rayukan maza 68 da mata uku, ya faru ne a ranar Lahadi a gundumar Bona, kamar yadda sanarwar da aka fitar ranar Lahadi da dare ta bayyana.
Wosenyeleh Simion, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama ya bayyana cewa fasinjojin baƙi ne waɗanda za su je wurin biki, inda wasu iyalan suka rasa mutane da dama.
Shi ma gidan talabijin na Ethiopia EBC ya ruwaito cewa fasinjojin suna hanyar zuwa wuri biki a lokacin da hatsarin ya faru.
Munanan haɗura
'Yan sandan da ke sa ido kan ababen hawa sun bayar da rahoton cewa motar ta yi lodi fiye da ƙima wanda hakan ne ake ganin ya jawo hatsarin.
"Akwai mutum biyar waɗanda ke cikin mawuyacin hali kuma suna karɓar magani a Babban Asibitin Bona," in ji shi.
Ana yawan samun munanan haɗuran mota a Ethiopia inda ba a sa ido kan yanayin tuƙi yadda ya kamata haka kuma ba a kula da motoci.
Ko a shekarar 2018 sai da mutum 38 waɗanda akasarinsu ɗalibai suka rasu bayan motar ta faɗo daga saman tsauni a arewacin Ethiopia.