Mahukuntan Moroko na yin gargaɗi game da 'tsananin zafi' da ake sa ran fuskanta a lardunan kasar da dama a makon nan, inda darajar zafin za ta kama tsakanin 42 da 46 a ma'aunin salshiyas.
Hukumar Kula da Yanayi ta ce tun daga ranar Litinin din nan tsananin zafin zai yi tasiri a yankunan da suka hada da Tata da Zagora da Assa-Zag da Es-Semara da Errachidia.
Sauran yankunan su ne Taounate da Ouezzane da Taroudant da Sidi Kacem da Sidi Slimane da Khemisset.
Tsananin zafi abu ne da aka saba gani a Moroko, amma mahukunta sun bayyana damuwa kan yadda lamarin ka iya janyo matsalar ruwan sha.
Sauyin yanayi
Ruwan sama ya ragu da kashi 70 a shekara, in ji Ma'aikatar Ruwa da Ayyukan Noma ta Moroko a watan Janairu.
Shekaru shida a jere na fari sun bar madatsun ruwa na Moroko a cikin mummunan yanayi, wanda hakan ya janyo raguwar yankunan da ake yin noman rani a cikinsu.
Ya zuwa tsakiyar watan Janairu, madatsun ruwa na Moroko sun cika da kashi 23.2 daga kashi 31.5 a shekarar da ta gabata, in ji Ministar Ruwa, Nizar Baraka.
Mummunan farin da aka samu a shekaru goman da suka gabata ne suka sanya aka hana wanke yankuna da ruwan sha mai tsafta ko yin ban ruwa a gonaki a filayen shaƙatawa a garuruwa.
Sannan an dakatar da amfani da ban ruwan wasu gonaki da ruwan madatsun ruwan.