Kungiyar ta ce akwai shanu sama da miliyan 20 a Nijeriya. Hoto/Getty Images

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar ta yi wa duka dabbobin kasar rigakafin cutar anthrax wadda aka samu barkewarta a Jihohin Neja da Legas.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa rigakafin ne kawai mafita ta magance wannan matsalar baki daya.

“Duk da cewa a jihohi biyu kawai aka bayar da rahoton barkewar cutar, hakan ba yana nufin ba za ta iya watsuwa zuwa sauran jihohi ba.

“Anthrax cuta ce da ke yaduwa tsakanin dabbobi da mutane kuma lamari ne da ya shafi tsaron kasa. Ganin yadda take bazuwa da jawo mace-mace, ya zama dole a magance ta cikin gaggawa,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta ce Nijeriya na da sama da shanu miliyan 20 da tumaki da awaki miliyan 75 kuma ana shiga da wasu kasar daga makwabtan kasashe.

“Mambobinmu sun yi asarar sama da shanu miliyan uku a rikicin da ake yi da satar shanu a fadin jihohi, ba mu shirya yin wata asara ba,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta jinjina wa gwamnatin Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya kan sayo rigakafin anthrax da za a yi wa duka dabbobin da ke jihar inda ta bukaci sauran jihohi su yi koyi da ita.

Matakan kariya daga cutar anthrax

Cutar anthrax da ake samu daga cin naman dabbobi takan nuna alamu kamar ciwon ciki, amai, tashin zuciya, ciwon kai, da gudawa mai zuwa da jini.

Dr. Sule Ali Gabas, wani likita a Sagmediconsult and Diagnostic Services Ltd, a Accra, ya bayar da wasu shawarwarin da za su taimaka wajen kauce wa wannan cuta.

  • Nisanta mu’amala ko taba dabbobin da suka kamu
  • Kaurace wa nama ko nono ko duk wani abu da ya fito daga dabba mara lafiya
  • Daina shiga yankin da cutar ta bayyana har sai an shawo kanta
  • Garzayawa asibiti idan an fuksanci alamu ko barazanar cutar.
TRT Afrika