Ministan Abuja babban birnin Nijeriya Nyesom Wike ya kafa wani kwamiti na musamman da zai sa ido kan kwararar almajirai cikin birnin.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja Olatunji Disu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai bayan gudanar da tattaunawa ta tsaro da ministan na Abuja.
Disu ya bayyana cewa Ministan Abujan ya ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa jami’an tsaro sun samu bayanai dangane da almajirai da abubuwan da suke gudanarwa a birnin daga ciki har da kula da su da kuma karatunsu.
Duk da cewa ya yi watsi game da tambayoyin da aka masa na barazanar tsaro a babban birnin, Disu ya buƙaci mazauna birnin su ci gaba da sa ido da kuma bayar da rahoto kan duk wani lamari da suka gani ba daidai ba.
Kwamitin ya ƙunshi ‘yan sanda da jami’an tsaron NCDC da jami’an DSS haka kuma an buƙaci ya bayar da rahoto nan da makonni biyu.
Tun bayan zamansa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fito da sabbin tsare-tsare wanda ya ce za su kawo ci gaba.
Daga ciki har da tilasta wa masu filaye a birnin biyan kuɗi domin samun takardar izinin mallakar filaye. Tuni ministan ya soke izinin filayen ɗaruruwan jama’a waɗanda ba su bi waɗannan ƙa’idoji ba.