Kwamitin Kare Hakkokin Ɗan'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Laraba don tsawaita binciken da ake yi na take hakkin bil adama a yaƙin da ake gwabzawa a Sudan, duk kuwa da ƙin amincewar Khartoum.
Ƙasashe 23 daga cikin mambobin majalisar 47 ne suka kada kuri'ar amincewa kan a tsawaita wa'adin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa a Sudan, inda 12 suka ki amincewa da shi, yayin da 12 su ka ƙaurace wa zaɓen.
Hukumar kare hakkin ɗan adama ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta gabatar da aikin binciken a watan Oktoban bara da nufin gudanar da bincike kan zarge-zargen take hakin 'yan adam da kuma keta dokokin jinƙai na kasa da kasa a rikicin.
Biritaniya da wasu ƙasashe da dama ne suka gabatar da wani daftarin ƙudurin a tsawaita wa'adin.
'Zalunci da rashin adalci'
"Daftarin ƙudurin, rashin adalci ne da kuma zalunci," kamar yadda jakadan Sudan Hassan Hamid Hassan ya shaida wa majalisar kafin soma kada kuri'ar.
"Yaya wani kuduri da wannan majalisar ta zartar zai dauki irin wannan matakin na rashin adalci, inda ake kwatanta halastacciyar rundunar sojojin kasar da ta 'yan tawaye masu tayar da kayar baya?"
"Wannan tsarin matakin bai dace ba kuma Sudan ba za ta amince da tsarin wannan ƙuduri ba," in ji shi.
Ƙasashen Argentina da Brazil da Faransa da Jamus da Japan da Afirka ta Kudu da kuma Amurka na daga cikin ƙasashen da suka kada kuri'ar amincewa kan a tsawaita lokacin.
China ta kada kuri'ar naƙi
Ƙasashen da suka kada kuri'a ƙin amince wa da ƙudurin sun hada da China, da Cuba, da Eritrea, da Indonesia, da Morocco, da Qatar da kuma ita kanta Sudan.
Aljeriya, da Bangladesh, da Indiya da Malaysia na daga cikin waɗanda suka ƙaurace wa zaɓen.
Tawagar aikin binciken mai mutane uku na karkashin jagorancin Mohamed Chande Othman, tsohon babban alkalin kasar Tanzaniya.
Yana tare da Joy Ezeilo, shugabar sashin shari'a a wata Jami'ar Nijeriya, da kuma Mona Rishmawi na Jordan da Switzerland, tsohuwar ƙwararriyar 'yancin ɗan adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya.
Tun a watan Afrilun 2023 ne yaƙi ya barke tsakanin sojojin ƙasar Sudan ƙarkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF), ƙarkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.