Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a ranar Lahadi kan kazamin rikicin da aka samu a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, bayan da Kinshasa ta janye jami’an diflomasiyyarta daga Kigali a daidai lokacin da ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda suka kai hari kan babban birnin Goma.
Lardunan gabashin Kivu mai arzikin albarkatun kasa na Arewaci da Kudancin Kivu sun shafe shekaru 30 suna fama da tashe-tashen hankula, inda kungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ta kasance daya daga cikin kungiyoyin masu dauke da makamai a shekarun baya-bayan nan.
Ta kwace yankuna da dama na gabashin DRC tun shekarar 2021, lamarin da ya raba dubbai da matsugunai tare da janyo rikicin bil adama.
Bayan da aka soke tattaunawar zaman lafiya tsakanin shugaban Rwanda Paul Kagame da Etienne Tshisekedi na DRC a tsakiyar watan Disamba, 'yan tawayen sun ci gaba da tunkarar Goma, babban birnin Kivu ta Arewa kuma wani muhimmin birni mai ɗauke da mutane fiye da miliyan daya.
A ranar Asabar, kasashe uku - Afirka ta Kudu, Malawi da Uruguay - sun sanar da mutuwar wasu sojojinsu 13 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin da ake fama da rikici.
Ta'azzarar rikicin ne ya sa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa, wanda tun da farko aka shirya yi a ranar litinin, wanda zai koma ranar Lahadi.