Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta sanya Sojojin Sudan da dakarun RSF cikin jerin '' 'yan ta'adda'' saboda ''kisa da raunata ƙananan yara da kuma kai hare-hare a makarantu da asibitoci.''
A wani rahoto na majalisar kan ''yara a yankunan da ke fama da riciki'' ya bayyana cewa tashe-tashen hankula da yara suke fuskanta a wuraren da ke fama yaki ya kai maƙura a shekarar 2023 musamman a Gaza da Sudan.
Kazalika ƙungiyar Hamas da sojojin Isra'ila su ma sun shiga cikin jerin masu aikata laifin yaƙi na MDD saboda yaƙin da suke yi da Hamas a Gaza.
"A shekarar 2023, cin zarafin ƙananan yara a wuraren da ke fama da tashe-tashen hankula ya yi tsanani sosai, inda aka samu ƙarin kashi 21 cikin dari a manyan laifuka,'' in ji rahoton Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres, wanda aka shirya wallafa shi a ranar Alhamis.
'Take hakkin ƙananan yara'
Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cin zarafin yara 30,705 a bara, waɗanda suka haɗa da kashe yara 5,301 tare da raunata 6,348, sai kuma yara 8,655 da aka ɗauka don amfani da su wajen kai hare-hare, sannan an hana yara 5,205 samun agajin jinƙai kana an yi garkuwa da 4,356.
"Ba mu taɓa samun bayanai kan cin zarafin ƙananan yara ba kamar na shekarar bara," a cewar wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya nemi a sakaya sunansa.
A shekarar 2023, ''Yara sun fuskanci wahalhalu iri daban-daban da kuma munanan tashe-tashen hankula da ke tattare da rashin mutunta hakkin yara, musamman hakkin rayuwa,'' in ji rahoton.
A tsakanin 2022 zuwa 2023 Sudan ta samu "ƙarin kaso 480 na ayyukan da suka shafin cin zarafin yara," a cewar rahoton na MDD.
Munanan hare-hare
An sanya dakarun RSF cikin jerin masu aikata laifi na ɗaukar yara tare da amfani da su wajen kai hari da yi musu ''fyaɗe da sauran nau'in cin zarafi,'' da kuma kai hare-hare kan makarantu da asibitoci.
"Na yi matukar kaduwa da karuwar cin zarafi mai tsanani kan yara, " kamar yadda Guterres ya rubuta a cikin rahoton, inda ya kuma bayyana ƙarin da aka samu a hare-haren ƙabilanci da kuma raba duban ƙananan yara da matsugunansu a Sudan.
Janyo hankalin duniya
Rahoton dai ya taoɓ yankuna 20 da ke fama da tashe-tashen a faɗin duniya, inda suka haɗa da yawan kashe-kashe da jikkata ƙananan yara da ɗaukarsu aiki da yin garkuwa da su da kuma keta hakkinsu.
Tuni dai MDD ta sanya sojojin Rasha da ''ƙungiyoyi masu alaƙa da ke ɗauke da makamai,'' cikin jerin waɗanda suka aikata manyan alaifuka na yaki saboda kashe yara 80 a Ukraine a shekarar 2023 tare da raunata 339.
Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya haifar da ƙaruwar cin zarafi kan yara da kashi 155, in ji rahoton.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da kashe ƙananan yara 43 a Isra'ila da gabar Yammacin Kogin Jordan a harin ranar 7 ga watan Oktoba, kazalika ƙungiyar Hamas da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa sun yi garkuwa da yaran Isra'ila 47.
Rahoton ya kuma tabbatar da mutuwar ƙananan yara Falasdinawa 2,141 a Zirin Gaza a shekarar 2023, yayin da a tsakanin ranar 7 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba na shekarar aka kashe yara 2,05.