Sojojin Sudan da mayaƙan rundunar RSF sun ƙaddamar da yaƙi da juna tun watan Afrilun 2023, lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum 20,000 tare da raba fiye da mutum miliyan 10 da muhallansu. / Hoto: Reuters Archive

Mutum aƙalla 124 sun mutu a harin da mayaƙan rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF) suka kai a ƙauyen Alseriha da ke jihar Gezira a tsakiyar Sudan, a cewar ƙungiyar likitoci ta Sudan Doctors Network.

“Dakarun RSF sun aiwatar da kisan kiyashi a kan fararen-hula 124 a ƙauyen Alseriha, a harin da suka kwashe sama da awa ɗaya suna kai wa a yankin, sannan sun jikkata ɗaruruwan jama'a tare da korar ɗaruruwa daga ƙauyen,” in ji sanarwar da ƙungiyar da ba ta gwamnati ba ta fitar ranar Asabar.

Ƙungiyar ta caccaki RSF kan hare-haren da ta kai ƙauyen Alseriha da ma wasu ƙauyuka da ke gabashi da yammacin Gezira, inda ta bayyana su a matsayin “na rashin hankali da aka kai kan fararen-hular da suka zaɓi su ci gaba da zama a inda suke duk da yaƙin da aka kwashe fiye da shelara ɗaya ana yi da kuma mawuyacin halin da suke ciki."

Rundunar RSF ba ta ce uffan ba game da wannan batu.

Tun da farko a ranar Juma'a, Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce magidanta da iyalansu fiye da 853 aka kora daga birnin Tamboul da ƙauyukan da ke jihar Gezira daga ranar 20 zuwa 24 ga watan Oktoban 2024, sakamakon ƙaruwar arangama tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan RSF.

AFP