Aƙalla masunta 20 ne mayaƙan Boko Haram suka kashe a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya bayan mayaƙan sun far wa ƙauyensu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato ‘yan sa-kai da mazauna ƙauyen suna cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 12 na rana lokacin da ‘yan Boko Haram suka buɗe wuta kan masunta da ke aiki a ƙauyen Gadan Gari.
Wani ɗan sa-kai, Modu Ari ya shaida wa Reuters cewa aƙalla mutum 20 ne suka mutu a lokacin da mayaƙan suka afka wa ƙauyen.
Kazalika Reuters ta ambato wani mazaunin ƙauyen, Mustapha Kachalla yana cewa ya rasa ɗa ɗaya a harin kuma an binne sama da gawawwaki 15 sakamakon harin.
Kawo yanzu dai gwamnati ko jami’an tsaro ba su ce komai game da lamarin ba.
Nijeriya ta shafe kimanin shekara 16 tana fama da rikicin Boko Haram wanda ya haddasa rasa rayukan dubban mutane da kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.