Tuggar ya  jaddada cewa yaƙin da ake yi akan mutanen Gaza ba zai zama daidai da Ƙa’idar Yaƙi na Adalci ba, kuma dole ne a dakatar da shi don kare bil'adama.

Gwamnatin Nijeriya ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen ci gaba da yin Allah wadai da yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza inda ake ta kashe mutane ba ƙaƙƙautawa a kowace rana.

Da yake jawabi a wajen taron Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai, OIC a Saudiyya, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce ƙasarsa ta yi maraba da shiga tsakanin da OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa (Arab League) suka ƙirƙiro.

“Nijeriya ta yi maraba da shiga tsakanin OIC da Arab League suka yi domin kara jaddada kiran da ake yi na kawo karshen cin zarafi da asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da ke jawo mummunan halin jinƙai,” Tuggar ya faɗa a wani bidiyo na taron, wanda ya wallafa a shafinsa na X.

Ko a ƙarshen watan Oktoba ma gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga a aiwatar da batun tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra'ila masu cin gashin kansu don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin bangarorin biyu.

OIC da Arab League sun shirya taron na ƙasashen Larabawa da kuma Ƙasashen Musulmai ne a ƙarshen makon da ya wuce a Saudiyya, don haɗuwa a lalubo bakin zaren yadda za a kawo ƙarshen zubar da jinin da ake yi a Gaza.

A cikin bidiyon mai tsawon munti huɗu, Tuggar ya ce “Mun hadu a cikin yanayi mai ban tausayi, a lokacin da hare-haren rashin hankali da ake ci gaba da kaiwa a Zirin Gaza ke sake sanya rayuwar bil'adama da fafaren hular da ba su ji ba ba su gani ba cikin barazana, da kuma haifar da bala'in jinƙai.”

Wakilin na Nijeriya a taron ya ƙara da cewa amfani da tsananin ƙarfi a kan al’ummar Gaza da ake yi yana bijiro da tambayar “ko mutum nawa za a ƙara kashewa nan gaba da sunan ɗaukar fansa.”

Bin koyarwar manyan addinai uku

Tuggar, ya ce ƙasarsa Nijeriya ta bi sahun sauran takwarorinta na duniya, musamman waɗanda suka halarci taron na Saudiyya wajen ganin laifin Isra’ila da aikata “zalunci” a kan Falasɗinawa.

Ya kafa misali da yadda dukkan addinai uku da suka fito daga tsatson Annabi Ibrahim suka shimfiɗa ƙa’idojin da gwamnatoci a cikin yanayi na yaƙi da juna.

“Rubuce-rubucen fitaccen masani Ibn Rushd a ƙarni na 12 a kan batun yaƙi ya yi tasiri sosai a kan mutane da dama ciki har da fitaccen masanin falsafa St Thomas Aquinas.

“Wannan aiki a dunƙule ya samar da ƙa'idar cewa gwamnatoci, (gwamnatocin da suka san me suke yi) suna amfani da su don sanin ko yaƙin zalunci ya dace da ɗabi'a,” Ambasada Tuggar ya shaida wa taron na OIC da ya samu halartar wakilan ƙasashen Musulmai da dama.

Ya jaddada cewa yaƙin da ake yi akan mutanen Gaza ba zai zama daidai da Ƙa’idar Yaƙi na Adalci ba, kuma dole ne a dakatar da shi don kare bil'adama.

Da ya taɓo batun yadda Isra’ila ke ta nanata wa duniya cewa da ƙungiyar Hamas take yaƙi, a matsayin kare kanta, Ministan na Nijeriya ya ce "tambayar da ya kamata mu yi wa kanmu ita ce, ina hujjar cewa tashin hankalin da Isra’ila ke yi a Gaza na yin wani mummunan tasiri ga Hamas?

Tuggar ya ce dole ne a haɗa kai don kawo ƙarshen rikicin da kuma lalubo mafita ta dindindin kan yaƙin Isra’ila da Falasɗinu ta hanyar bin matsayar Majalisar Ɗinkin Duniya ta samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.

“A kan wannan matsayar Nijeriya ta tsaya a ƙyam,” ya faɗa.

TRT Afrika