Ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewacin Nijeriya da ƙungiyar sarakunan gargajiya na yankin sun gudanar da wani taro a ranar Litinin inda suka tattauna kan matsalolin da ke addabar da yankin.
Taron wanda aka yi shi a Kaduna ya kuma samu halartar Babban Hafsan Rundunar Tsaro na Nijeriya Janar Christopher Musa, wanda ya yi bayani a kan ƙalubalen tsaro da arewacin ƙasar ke fama da su.
Bayan kammala taron, ƙungiyoyin biyu sun fitar da wata sanarwa inda suka bayyana abubuwan da suka tattauna kuma suka amince za a magance su kamar haka:
1. Ƙungiyar gwamnonin ta jajanta wa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Maiduguri da sauran sassan Arewa, da iyalan wadanda bala'in gobrarar tanka mai ta shafa a jihar Jigawa da sauran wadanda ta’addanci da makamantansu ya shafa a Arewa da Nijeriya baki. Shugabannin sun amince da ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi don ba da tallafin da ya kamata ga wadanda abin ya shafa.
2. Ƙungiyar ta jaddada cewa, Masarautun Gargajiya na da matukar muhimmanci wajen neman dauwamammen zaman lafiya da tsaro a yankin. Ta kuma amince da ƙudurin ɗinke barakar da ke tsakanin gwamnati da jama’a. Sannan ta ba da shawarar a ƙara wa masarautun gargajiya damar taka rawar gani don haɓaka haɗin gwiwa da hukumomin tsaro don yaƙi da satar mutane, fashi da makami, satar shanu, rikicin kabilanci, rikicin manoma da makiyaya da sauran laifuka.
3. Dandalin ya amince da nasarorin da aka samu a baya-bayan nan kan masu laifi, musamman kawar da ‘yan fashi da shugabannin ta’addanci. Duk da haka, mun yanke shawarar samun ɗorewar wadannan nasarorin ne don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ƙungiyar ta yaba wa Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro da Janar Christopher Musa bisa jajircewar da suka yi wajen ganin al’umma tana cikin aminci. "Amma duk da haka akwai bukatar a ƙara ƙaimi domin magance matsalolin da ke addabar yankin Arewa."
4. Kan batun zanga-zangar "End Bad Governance" da aka yi a cikin watan Agusta, ƙungiyar ta yanke shawarar ƙara yunƙurin magance matsalolin da ke haifar da tashe-tashen hankulan matasa ta hanyar saka hannun jari a fannin ilimi, haɓaka sana'o'i, samar da ayyukan yi don inganta rayuwarsu da kawar da hankulansu daga munanan ɗabi'u.
5. Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta magance matsalar wutar lantarki da ke addabar yawancin Jihohin Arewa sakamakon ɓarnatar da kayayyakin wutar lantarkin. "Wannan al'amari ba wai kawai yana nuna raunin muhimman ababen more rayuwa ba ne, har ma da bukatar samar da hanyoyin sadarwa na zamani da samar da wutar lantarki dauwamammiya a yankin."
6. Dandalin ya amince cewa Arewacin Nijeriya yana da dimbin albarkatun noma, wanda idan aka yi amfani da shi sosai, zai iya rage yunwa da bunkasar tattalin arziki. "Don cim ma wannan burin, mun kuduri aniyar bayar da tallafin da ya dace ga manomanmu, da suka hada da samar da kudade, dabarun noma na zamani da ababen more rayuwa kamar tituna da na ban ruwa. Za a kalli noma a matsayin hanyar ciyar da al'ummar da samar da masana'antu da samar da ayyukan yi a fadin yankin."
7. Dandalin ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa shirin kawo sauyi a bangaren kiwo tare da amincewa da samar da kudirin siyasa da jajircewa wajen ganin an samu nasara.
8. Ƙungiyoyin biyu sun amince cewa sauyin yanayi ya yi matukar tasiri ga muhalli wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a sassan Arewa da dama a baya-bayan nan, don haka sun ƙuduri aniyar yin hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen gina magudanan ruwa da madatsu don karkatar da ruwan da ya wuce ƙima da samun damar noman rani.
9. Ƙungiyar gwamnonin ta amince da tallafawa da kuma shigar da duk wani shiri da nufin magance kalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta da inganta sakamakon ilimi a yankin.
10. Dandalin ya yi tsokaci kan abin da ke cikin kudurin dokar sake fasalin haraji da aka miƙa wa majalisar dokokin kasar, musamman ma yin nazari kan tsarin harajin da ya saɓa wa muradun arewa. Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, taron ya yi watsi da gyaran harajin da ake shirin yi, tare da yin kira ga ‘yan majalisun dokokin kasar da su yi adawa da duk wani kudiri da zai kawo cikas ga rayuwar al’ummarsu.
11. "Don kauce wa shakku, kungiyar Gwamnonin Arewa ba ta ƙyamar duk wasu manufofi ko shirye-shiryen da za su tabbatar da ci gaban kasar nan. Duk da haka, dandalin ya yi kira da a yi adalci da gaskiya wajen aiwatar da dukkan manufofi da tsare-tsare na kasa don tabbatar da cewa babu wani yanki na siyasa da za a nuna wa wariya."
12. A halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ke fama da shi, kungiyar ta yi kira ga daukacin ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, "domin kuwa jihohi da gwamnatin tarayya suna bakin kokarinsu wajen aiwatar da matakan da za su daƙile matsalar."