Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa a karon farko ya fitar da man fetur zuwa Kamaru, wanda hakan ake sa ran zai buɗe wata hanya da za ta taimaka wurin samun wadataccen man fetur da kuma daidaita farashi a yankin.
Sai dai kamfanin na Dangote bai bayar da cikakken bayani kan ganga nawa aka fitar ba.
Kamfanin samar da makamashi na kasar Kamaru Neptune Oil a cikin wata sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa, dukkanin kamfanonin biyu suna nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a fadin yankin.
Neptune Oil ya ce an aiwatar da cinikin samar da man ba tare da masu shiga tsakani ba.
Matatar man ta Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kullum na da burin yin gogayya da matatun mai na Turai idan ta soma aiki gadan-gadan.