An tura daya daga cikin matasan sashen binciken kisan kai domin cigaba da gudanar da bincike. Hoto/Nigeria Police Force

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ta kama wasu matasa kan zargin kashe iyayensu, inda daya ya buga wa mahaifinsa tabarya a Abuja, daya kuma ya caka wa mahaifiyarsa wuka a Kano.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin kasar Josephine Adeh ta tabbatar wa TRT Afrika cewa an kama wani matashi mai suna Emmanuel John kan zarginsa da kashe mahaifinsa.

Emmanuel ya buga wa mahaifinsa Mista Monday tabarya a lokacin da marigayin ke fada da mahaifiyarsa.

“Mahaifinsa yana dambe da mahaifiyarsa, sai yaron ya goyi bayan mahaifiyarsa inda ya dauki tabarya ya buga wa mahaifinsa a kai, sai ya rasu,” in ji Josephine.

Ta tabbatar da cewa tun ranar 2 ga watan Mayu aka kama matashin, mai shekara 16, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kwana daya da faruwar wannan lamari ne ita ma rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta bayyana cewa wani matashi ya kashe mahaifiyarsa a jihar inda ta ce tana nemansa ruwa a jallo.

Kwana guda bayan hakan ‘yan sandan suka ce sun kama matashin mai suna Ibrahim Musa.

‘Yan sandan sun ce matashin, mai shekara 22, ya kashe mahaifiyarsa Hajara Muhammad, mai shekara 50, ta hanyar caka mata wuka a sassa daban-daban na jikinta a rukunin gidaje na Rimin Kebbe da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa an kama matashin a Dawakin Tofa da ke Kano bayan ya tsere.

“A bincike na wucin-gadi da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya amsa cewa yana tu’ammali da miyagun kwayoyi,” kamar yadda SP Kiyawa ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa na jawabi kan lamarin.

“An tura sa babban sashen binciken manyan laifuka bangaren kisan kai domin gudanar da bincike, bayan haka za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin a yi masa hukunci,” in ji Kiyawa

TRT Afrika