Hukumar kula da bayar da rahotannin yanayi ta Nijeriya, wato Nigerian Meteorological Agency (NiMET), ta gargadi mazauna wasu jihohi game da fuskantar yanayin zafi a awon sama da digiri 40 a ma’aunin salshiyas har na tsawon kwana biyu.
Hukumar ta wallafa wannan gargadi ne a shafinta na Tuwita ranar 26 ga watan Maris, inda ta bayyana cewa ana sa ran fuskantar matsanancin yanayin “cikin awa 48 masu zuwa”.
Sanarwar ta ayyana biranen Bauchi da Gombe da Borno da Yola a matsayin wadanda suke cikin hadarin fuskantar tsananin zafi mai sa takura.
Hakanan, cikin kwanakin da za su biyo baya, ana hasashen wasu yankunan Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa, za su tsinci kansu a yanayin zafi sama da digiri 40 a ma’aunin salshiyas.
Kari kan wannan, gargadin ya ambaci cewa wasu yankunan kamar Kwara da Abuja da Binuwai za su iya fuskantar zafi digiri 35 zuwa 40 a ma’aunin salshiyas.
Hasashen hauhawar yanayin zafi tsakanin wadannan jihohi zai iya haifar da abin da NiMET ta kira da “zafi mai sa takura”, wanda wani nau’in yanayi ne mai sa takura da kuma hadarin cututtuka da ke samuwa ta dalilin zafin yanayi.
Sai dai kuma, tasirin “zafi mai sa takura” ya dogara ne kan shiga cikin zafin, da tsinkaye, da sabo, har da yanayin tunani da zamantakewar mutane.
NiMET ta bayar da shawara ga mutanen da ke zama a yankunan da ke fuskantar barazanar “su dinga shan abubuwa masu ruwa-ruwa sosai cikin irin wannan yanayi”.
Hasashen tsanantar zafin ya zo ne a lokacin da Musulmai suke azumtar watan Ramadana.
Da yake magana da TRT Afrika, Sheik Muhammad Bin Uthman, wani malamin addinin Musulunci da ke birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya shawarci Musulmai su sha ruwa sosai a lokacin yin sahur da buda baki.
Ya ce "Wannan zai rage musu tsananin kishirwar da ka iya shafar walwalarsu a yayin da suke azumi a yanayin tsananin zafi”.
Ya kara da cewa, “A yanayi na matukar takura, ya halatta Musulmi ya karya azuminsa idan azumin zai iya zamowa hadari ga lafiya ko rayuka, musamman idan karya azumin shi ne kadai mafita gare shi”.
Kwararru a harkar lafiya sun nuna damuwa kan wannan lamari saboda yowuwar barkewar cututtuka masu alaka da zafi a tsakanin al'umma a kasar.
Yawanci a lokutan tsananin zafi a kan samu barkewar cututtuka irin su sankarau da amai da gudawa da sauran su.