An kashe sama da mutum 10,328 a Gaza tun bayan soma wannan rikicin. Hoto/Kawu Sumaila

‘Yan Majalisar Dattawan Nijeriya sun tafka muhawara a ranar Talata bisa rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Wannan na zuwa bayan Isra’ila ta shafe wata guda tana kai wa Gaza hari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 10,328.

‘Yan majalisar dattawan sun yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta dauki matakan gaggawa ta hanyar hada kai da sauran kasashe domin kawo karshen wannan rikici domin ceto rayukan jama’a da dukiyoyi.

Tun da farko Sanata Suleiman Kawu Sumaila daga Kano ne ya dauki nauyin wannan kudirin tare da hadin kan sanatoci 28.

Sanata Adamu Aliero ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa inda ya bukaci majalisar ta sa baki domin gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan tsarin kafa kasashe biyu, wato “two-state solution” ga Falasdinawa da Isra’ila.

Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Barau Jibrin ba a bar shi a baya ba a wannan muhawara inda ya bayyana cewa abin da ake bukata a halin yanzu shi ne tsagaita wuta.

“Abubuwan da ake gani a talabijin a yanzu su ne gawarwaki da sauransu. Ba za a yarda da wannan ba. Wannan bai dace da duniya a wannan zamanin ba,” in ji shi.

A nasa bangaren, Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce ganin cewa yana sane da yadda yakin basasa yake sakamakon ya fuskance shi tun yana yaro, rikicin ba zai samar da wata hanya mai bullewa ba, in ji shi.

Akasarin ‘yan majalisar sun amince da wannan kudirin. Shugaban majalisar Godswill Akpabio daga baya ya bukaci akawun majalisar ya tura wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu matsayar majalisar kan batun na Gaza da Isra’ila.

Tuni gwamnatin Nijeriyar ta soma daukar mataki inda ta soke ziyarar da Firaiministan Jamhuriyar Czech Petr Fiala da tawagarsa ta 'yan kasuwa za su kai kasar.

Ana ganin matakin na da nasaba da matsayar Jamhuriyar Czech na goyon bayan Isra'ila a hare-haren da take ci gaba da kai wa Falasdinawa.

TRT Afrika