Masu bincike sun gano wani sabon jinsin kakannin ƙadangaru a Zimbabwe, kamar yadda wata sabuwar mujallar kimiyya da aka wallafa ta bayyana.
Wata tawaga daga jami'o'in Witwatersrand da Stony Brook tare da Hukumar Gidajen Adana Kayayyakin Tarihi da aka Haliita ta Zimbabwe, da Gidan Adana Kayana Tarihi da aka Halitta ta London ne suka yi aikin.
Masana kimiyyar sun gano ƙasusuwan ne a gefen tafkin Kariba da ke kusa da iyakar ƙasar Zimbabwe da Zambia, waɗanda aka yi ƙiyasin sun kai shekara miliyan 210.
Sakamakon, wanda aka buga a mujallar Acta Palaeontologica Polonica ranar Alhamis, ya nuna wasu abubuwa na daban da suka bambanta su da sauran nau'in kakannin ƙadangaru da aka sani a wancan zamanin.
An danganta wannan nau'in da rukunin farko na kakannin ƙadangaru, da aka sansu da dogon wuya, da kuma amfani da tsirrai a matsayin abinci, sannan an sa mata suna Musankwa sanyatiensis
Wannan shi ne karo na huɗu da ake gano kakannin ƙadangaru a Zimbabwe, kuma na nuna irin albarkatun da yankin ke da shi wanda za a iya faɗaɗa bincike na tarihi kan rayuwar tsirrai da kashin dabbobin da suka shuɗe tsawon tarihi.