Wata babbar tawagar gwamnatin Amurka ta bar Nijar bayan ta gaza ganin shugaban mulkin sojin ƙasar, Abdourahamane Tiani, kamar yadda aka shirya a baya, a ɓangaren Amurka.
Ziyarar ta kwana uku, wadda ta zo ƙarshe ranar Alhamis, ta yi yunƙurin sabunta alaƙa da gwamnatin sojin da ta hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnati a ƙasar ta Yammacin Afirka, wadda tuni ta fara gina alaƙa a Rasha.
"Tawagar ta Amurka ta bar birnin Yamai ranar Alhamis bayan tattaunawa da wasu jami'an Nijar, ciki har da Firaminista Ali Mahaman Lamime Zeine," a cewar wata majiyar diflomasiyya.
Wata majiyar gwamnatin Nijar ta ce, tawagar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen sashen Afirka, Molly Phee, an shirya za ta zauna a Yamai tsawon kwana biyu, amma sun tsawaita zamansu da kwana ɗaya.
Rundunar sojin Amurka a Nijar
Janar Michael Langley, kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka, yana cikin tawagar.
Har yanzu Amurka tana girke da sojoji kusan 1,000 a Nijar a wani sansani da ke hamada, wanda aka gina a kudi da ya kai dala miliyan $100, duk da dai ayyukan sansanin sun taƙaita tun bayan juyin mulkin, kuma gwamnatin Amurka ta rage tallafin da take bai wa gwamnatin Nijar.
Sakataren Wajen Amurka, Antony Blinken ya kai wata ziyarar da ba a saba gani ba zuwa Nijar, watanni huɗu kafin soji su kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum kuma suka masa ɗaurin talala.
Sojin Nijar sun ta da jijiyar wuya kan tsohuwar ƙasar da ta musu mulkin mallaka, wato Faransa, inda ta tilasta wa sojin Faransa barin ƙasar bayan sun zauna tsawon kusan shekaru 10.
Sai dai gwamnatin sojin Nijar, wadda ta yi aiki tare da Amurka a baya, ba ta nemi fitar da sojin Amurka daga ƙasar ba.
Amma sojin Nijar sun nemi haɗin-kai da Rasha, duk da ba su kai ga rungumar Rasha gabaɗaya ba, kamar yadda maƙotan Nijar, Mali da Burkina Faso suka yi ba.