Ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa sun kassara rayuwar jama'a a Abidjan. / Hoto: AFP Archive

Ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas a Abidjan, babban birnin Cote d'Ivoire bayan wani mamakon ruwan sama da aka sheƙa, kamar yadda hukumar kashe gobara ta ƙasar ta bayyana ranar Asabar.

Hanyoyi sun lalace a yayin da aka sheƙa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ranar Alhamis da yamma a galibin yankunan birnin mai kimanin mutum miliyan shida.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar kashe gobara ta ce an kai mutum 18 asibiti.

An soma mamakon ruwan saman ne ranar Alhamis zuwa ranar Asabar da safe.

An tafka ruwan da ya kamata ya sauka daga watan Mayu zuwa Yuli — wato milimita 214 (inci 8.4) — a cikin awa 24, a cewar hukumar kula da yanayi ta ƙasar mai suna Sodexam.

A shekarar da ta wuce, mutum aƙalla 30 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da sauran bala'o'i da ke da alaƙa da ruwan sama.

AFP