Magoya bayan gwamnatin sojin Mali sun yi zanga-zangar nuna adawa da kungiyar ECOWAS a Bamako / Hoto: Reuters

Rundunar sojin Mali ta yi watsi tare da karyata rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da ya bayyana cewa dakarun kasar tare da taimakon sojojin ketare sun yi wa fararen-hula akalla 500 kisan gilla a yayin ayyukansu na yaki da ta’addanci a kasar a 2022.

Sojojin su fitar da sanarwar ce kwana guda bayan fitowar rahoton MDD da aka dade ana jira kan abubuwan da suka faru a tsakiyar garin Moura tsakanin ranakun 27 zuwa 31 ga Maris na 2022.

"Babu wani farar-hula daga Moura da ya rasa ransa a yayin farmakin da soji suka kai," in ji sanarwar da kakakin gwamnati, Kanal Abdoulaye Maiga ya karanto a gidan talabijin na kasar.

"Mayakan 'yan ta'adda ne kawai suka mutu."

Yayin da take Allah wadai da abin da ta kira "rahoton nuna son kai bisa ga wani labari na kage", gwamnatin ta bayyana mamakinta kan yadda rahoton binciken da MDD ta yi wajen amfani da tauraron dan adam a Moura wajen tattara bayananta, ba tare da izinin gwamnati ba.

Sanarwar ta kara da cewa hakan tamkar kaddamar da wani binciken leken asiri ne da kai hari kan jami'an tsaron kasar da kuma " makarkashiya kan harkokin soji".

Kagen rahotanni

Alkaluman da hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ta fitar sun bayyana cewa kisan gillan da aka yi a Mali shi ne mafi munin tashin hankali da kasar ta fuskanta tun bayan ta’azzarar hare-haren ta’addanci a sassan kasar a 2012.

Babban Kwamishinan kare hakkin bil adama na MDD, Volker Türk, ya ce sakamakon binciken ya matukar ta da hankali inda ya nuna "danyen hukuncin aika-aikar da Sojojin Mali da taimakon sojin ketare ke yi wa jama’ar kasar ta hanyar azabtarwa da kisan gilla da fyade kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya kai laifukan cin zarafin bil'adama".

Turk ya bukaci mahukunta a Mali da su mutunta ka'idojin dokokin jinkai na kasa da kasa da kuma dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa a lokacin da suke gudanar da duk wani aiki na tabbatar da doka da oda na soja.

Rahoton dai shi ne mafi muni da aka taba fitarwa kan sojin Mali da kawayenta na kasashen waje.

Duk da cewa rahoton bai fito karara ya bayyana sunan kasar da sojojin ketaren da suka taimaka wa Malin suka fito ba, sai dai an ga 'yan Rasha sun shigo kasar inda kasashen yammaci da wasu ke cewa zargin cewa sojojin haya ne na kamfanin tsaro na Wagner mallakin kasar.

TRT World