An yi ta jin karar harbe-harbe a kan titunan Bamako, babban birnin kasar Mali, da sanyin safiyar Talata, kamar yadda mazauna garin suka ce. / Hoto: Reuters

Wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a wata cibiyar horas da Jandarmomi a Bamako babban birnin kasar Mali a safiyar Talata, amma yanzu an shawo kan lamarin, in ji sojojin ƙasar.

Rundunar Sojin Mali ta ce wasu ‘yan ta’adda sun yi yunkurin kutsawa cikin makarantar Faladie Gendarmerie da ke Bamako babban birnin kasar.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa gawarwakin na kwance a kusa da wani sansanin Jandarma da ke Bamako babban birnin kasar Mali bayan harin.

Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ji karar fashewar wasu abubuwa guda biyu sannan ya ga hayaki na tashi daga nesa. Makarantar horarwar tana bayan gari.

‘Yan bindigan da ba a san ko su wane ne ba

Ba a dai san ko su waye maharan ba, ko su nawa ne ba haka kuma ko an shawo kan lamarin.

An yi ta jin karar harbe-harbe a kan titunan Bamako, babban birnin kasar Mali, da sanyin safiyar Talata, kamar yadda mazauna garin suka ce.

Da sanyin safiyar Talata ne aka yi ta jin karar harbe-harbe a wasu yankuna na Bamako babban birnin kasar Mali.

An ji ƙarar harbe-harben bindigar a unguwar Banankabougou.

Mutanen da ke hanyar zuwa masallaci domin gudanar da sallar Asubah sun juya sun koma gidajensu sakamakon ƙarar bindigar.

Mutanen sun bayyana cewa harbin bindigar ya fara ne da misalin ƙarfe 5:30 na Asuba.

Kasar Mali dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da dama da ke yaki da ‘yan tawaye masu iƙirarin jihadi da suka adabbi arewacin ƙasar tun daga shekara ta 2012, kuma tun daga nan suka bazu a yankin Sahel da kuma a baya-bayan nan zuwa arewacin kasashen da ke gabar teku.

Dubban mutane ne aka kashe tare da raba miliyoyi da muhallansu a yankin a daidai lokacin da sojojin ƙasar ke ƙoƙarin yaƙar 'yan ta'addan, inda ake zargin gwamnatoci da mayaka da cin zarafin fararen hula.

Bacin rai ga hukumomi na kasa maido da tsaro ya taimaka wajen juyin mulki sau biyu a Mali - a 2020 da 2021 - biyu na makwabciyarta Burkina Faso da daya a Nijar.

Bacin rai na rasa kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar ya jawo juyin mulki sau biyu a Mali - a 2020 da 2021 – inda maƙwabtan ƙasar biyu su ma suka biyo baya da juyin mulki wato Nijar da Burkina Faso.

Reuters