Ƙungiyar Ƙasashen Yankin Sahel za ta bullo da sabbin fasfo din ƙasashensu uku. / Hoto: Reuters

Shugaban kasar Mali ya bayyana cewa kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su bullo da sabbin fasfo din tafiye-tafiye a wani bangare na ficewarsu daga Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka domin kafa sabon ƙawancen yankin Sahel bayan da shugabannin sojoji suka karbe mulki a dukkan kasashen uku.

Makwabtan yankin Sahel da ke karkashin mulkin sojan guda uku a cikin watan Janairu sun sanar da cewa za su fice daga kungiyar ECOWAS mai mambobi 15, wadda ta yi kokarin shawo kansu su sake yin la'akari da shawarar da suka yanke.

A farkon wannan watan ne Burkina Faso ta sanar da cewa za ta fitar da sabon fasfo ba tare da tambarin ƙungiyar ECOWAS ba.

"A cikin kwanaki masu zuwa, za a yi amfani da sabon fasfo na AES (Alliance of Sahel) da nufin daidaita takardun balaguro a yankinmu da kuma saukaka zirga-zirgar 'yan kasarmu a duk fadin duniya," in ji shugaban mulkin sojan Mali, Assimi Goita, kamar yadda ya sanar da yammacin Lahadi.

Haɗin gwiwa wajen watsa labarai

Ya yi magana ne gabanin wata ganawa da Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen uku za su yi a ranar Litinin, dangane da zagayowar ranar da suka yanke shawarar kafa kawancen nasu.

Goita ya kuma ce suna shirin ƙaddamar da wata kafar yada labarai ta intanet "domin inganta yada labarai cikin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashenmu uku."

Kungiyar ECOWAS ta yi gargadin cewa ficewar kasashen ukun zai gurgunta 'yancin walwala da kuma kasuwar bai daya ta mutum miliyan 400 da ke rayuwa a ƙasashen ƙungiyar mai shekaru 49.

Ficewar tasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin ƙasashen nasu ke fafatawa da kungiyoyin da ke dauke da makamai, wadanda rikicinsu ya janyo tabarbarewar al'amuran yankin cikin shekaru goma da suka gabata, tare da yin barazanar bazuwa cikin Ƙasashen Yammacin Afirka da ke gabar teku.

Reuters
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince