Malawi ta tsananta neman mutanen da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su a cikin ruwa

Malawi ta tsananta neman mutanen da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su a cikin ruwa

Jirgin na C2110 ya taso ne daga Tafkin Nkhotakota inda ya nufi gabashin Malawi kana ya yi hatsari mintuna 45 kafin saukarsa.
 An hango tarkacen jirgin a karkashin ruwa kusa da gabar teku / Hoto: Reuters  

Hukumomi a Malawi sun tsananta aikin ceto bayan da wani jirgin sama mallakin wasu 'yan ƙasar Netherland su biyu ya yi hatsari a cikin tafkin ruwan ƙasar a yammacin ranar Talata.

Jirgin na wani kamfanin ƙasar Zimbabwe ne mai suna Nyasa Express kana matukin jirgin ɗan kasar Zimbabwe ne.

Wasu masunta sun ceto wata mata yar ƙasar Netherland daga cikin fasinjojin jirgin, kuma a halin yanzu tana asibiti tana samun kulawa.

Ministan yada labarai da ci gaban zamani na Malawi Moses Kunkuyu ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Anadolu a ranar Laraba cewa gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen neman sauran mutane biyun da suka ɓata - fasinja ɗaya ɗan Netherland da kuma matukin jirgin ɗan Zimbabwe.

''Muna da ƙwarin gwiwar cewa, zuwa yammacin ranar Laraba, za mu iya samun nasara a aikin da ceton da muke yi,'' in ji shi.

Gano tarkace jirgin

Jirgin na C2110 ya taso ne daga Tafkin Nkhotakota inda ya nufi gabashin Malawi kana ya yi hatsari a mintuna 45 kafin ya saukarsa.

“Ana ƙoƙarin ganin an fito da sauran tarkacen jirgin zuwa bakin tekun, a halin yanzu an hango su a ƙarƙashin ruwa kusa da gaɓar tekun,'' in ji Kunkuyu.

A ranar 10 ga watan Yuni, wani hatsarin jirgin sama ya kashe mataimakin shugaban ƙasar Malawi Sailosi Klaus Chilima da wasu mutum takwas.

Har yanzu dai ana kan gudanar da bincike don gano musabbabin abin da haifar da hatsarin jirgin.

AA