Sojojin na Nijar sun kwace iko da gwamnatin kasar tun a ranar 26 ga watan Yuli. Hoto/Others

Shugaban kungiyar malaman jami'oin Jamhuriyar Nijar, SNEC, ya ce takwarorinsa da sojojin kasar suka kama sakamakon adawa da juyin mulki suna cikin koshin lafiya.

Malam Na’bala Adare, wanda ya bayyana haka a hirarsa da TRT Afrika, ya tabbatar da cewa malaman da aka kama sun kai 43.

A cewarsa, ana ci gaba da tsare su a ofishin rundunar ‘yan sandan farin-kaya wato PJ inda ake binciken su a kan “wasu laifufukan na daban.”

“Mun je mun gan su a inda ake tsare da su kuma cikin koshin lafiya. Wannan batu ne da ya shafe su da sojoji, ba shi da dangantaka da kungiyar malaman jami’a,” in ji shi.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun nada ministoci 21

Malam Na’bala Adare ya kara da cewa an kama malaman ne bayar sun fitar da wata wasika da ke adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi.

Ya kara da cewa yawancin lakcarorin da aka kama makusantan hambararriyar gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ne, wasu ma ‘yan jam'iyar PNDS da aka tumbuke ne.

“Yawancinsu sun rike da mukaman mashawarta a fadar shugaban kasa da ofishin firaiminista da ofisoshin ministoci a gwamnatin da aka hambarar,” a cewar Malam Na’bala Adare.

Sojojin su kama jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar da aka cire daga kan mulki tun bayan da suka yi juyin mulki ranar 26 ga watan Yuli.

TRT Afrika