Sojojin Gabon sun sanar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin sabon shugaban kasar. / Hoto: AFP

Ana sa ran kasashe makwabtan Gabon za su yi wani taro na musamman bayan da sojoji suka hambarar da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, tare da yi masa daurin talala.

Sai dai ba a sanar da lokaci da wajen da za a yi tarin ba na Kungiyar Kasashen Tsakiyar Afirka (ECCAS), amma ta yi kira da a yi gaggawar mayar da doka da oda a kasar, a cewar sanarwar da ta fitar.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da amfani da karfi wajen warware rikicin siyasar kasar tare da kwace iko.

Sojojin Gabon sun sanar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin sabon shugaban kasar.

Zabe mai magudi

Shugaban harkokin waje na Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce ba za a iya kwatanta juyin mulkin Gabon da rikicin da ke faruwa a Nijar ba, yana mai cewa a Gabon sojojin sun kai dauki ne bayan da Shugaban Ali Bongo ya lashe zaben da ake ganin yana cike da magudi.

"A zahiri juyin mulki ba mafita ba ce, amma kar mu manta cewa a Gabon an yi zabe ne mai cike da magudi da ba sahihi ba," ya fada a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa magudin zabe ka iya jawo "juyin mulkin."

Borrell yana magana ne abanin taron ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai inda za su tattauna yadda za su taimaki kungiyar ECOWAS kan yadda za ta shawo kan juyin mulkin da aka yi ranar 26 ga watan Yuli a Nijar.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin baya-bayan nan kuma manyan kasashen nahiyar masu karfi irin Nijeriya sun bayyana fargabar yadda "juyin mulki ke wastuwa" a Afirka ganin irin yadda hakan ya faru a Nijar da Mali.

TRT Afrika