Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres ya “damu matuka” game da rahotannin harin da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) suka kai birnin Al Fasher na kasar Sudan.
Guterres ya yi gargadin cewa duk wani ci gaba da yaɗuwar yakin, zai iya yin barazanar afkawar yankin Darfur na yammacin kasar cikin yakin, a cewar kakakin MDD a ranar Asabar.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce, Guterres "ya yi kira ga Laftanar Janar Mohamed Hamdan 'Hemetti' Dagalo da ya dauki matakin da ya dace kuma ya ba da umarnin dakatar da harin na RSF.
"Ba daidai ba ne yadda bangarorin da ke yaƙi da juna suka yi watsi da kiraye-kirayen a daina tashin hankalin."
Yaki ya barke a Sudan tsakanin sojojin Sudan da RSF a watan Afrilun bara, wanda ya haifar da matsalar raba mutane da mahallansu mafi girma a duniya.
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin barkewar tashin hankalin da ke faruwa a kusa da Al Fasher na barazanar sake haifar da rikicin kabilanci.
UAE 'tana tallafawa' RSF
Babban Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na Amurka Jake Sullivan ya fada a ranar Asabar cewa, rikicin na Sudan zai kasance cikin abin da za a tattauna yayin da shugaba Joe Biden ya gana da shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a ranar Litinin.
Sudan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi musayar yawu a Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya kan zargin da gwamnatin soja ta Sudan ta yi cewa, UAE na bai wa kungiyar RSF makamai da goyon baya.
Sullivan ya shaida wa manema labarai cewa "Mun damu kan kasashe da dama da irin matakan da suke dauka na ta'azzara lamari a maimakon kawo ƙarshen rikicin."
"Babbar manufarmu ita ce mu dora rikicin da Sudan bisa wata turba ta daban fiye da mummunan turbar da ya ke a yanzu. Kuma ina ganin hakan na bukatar tattaunawa mai zafi amma mai cike da diflomasiyya da ɓangarori da dama da ke da ruwa da tsaki."
A wani kuduri da aka amince da shi a watan Yuni, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci dakatar da killace Al Fasher - birnin da ke da mutane miliyan 1.8 a yankin Darfur ta arewacin Sudan - da kungiyar RSF ta yi, da kuma kawo karshen fadan da ake yi a yankin nan-take.
Kudurin ya kuma yi kira da a janye dukkan mayakan da ke barazana ga tsaro da rayuwar fararen hula a Al Fasher, wanda shi ne babban birni na ƙarshe a yankin Darfur da ba ya ƙarƙashin ikon RSF.