| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su bincike El-Rufai
Rahoton binciken da aka gabatar a gaban majalisar ya zargi El-Rufai da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa da cin amanar aiki da halasta kuɗin haram da cin bashi ba bisa ƙa'ida ba.
Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su bincike El-Rufai
Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Zacharia. / Hoto: El Rufai / Others
5 Yuni 2024

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan jihar Nasir El Rufai da wasu muƙarraban gwamnatinsa kan zargin cin amanar aiki da halasta kuɗin haram.

Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Zacharia.

A cewar rahoton da Zacharia ya gabatar a ranar Laraba, yawancin bashin kuɗin da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su yadda suka dace, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun bashin ba.

Don haka kwamitin ya bayar da shawara ga hukumomin yaƙi da rashawa su gudanar da bincike da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu jami’an gwamnatin kan zargin amfani da mukami domin bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba, da karkatar da kudaden jama’a, da kuma kudade.

MAJIYA:TRT Afrika