Ranar 7 ga Janairun nan ne aka rantsar da Shugaba John Mahama a matsayin shugaban ƙasar Ghana / Hoto:Reuters

Majalisar dokokin Ghana ta amince da rukunin farko na sunayen ministoci da shugaban ƙasar John Mahama ya tura mata domin tantancewa.

Ministocin da majalisar ta amince da su sun da haɗa da Dr Cassiel Ato Bah a matsayin Ministan Kuɗi; da John Abdulai Jinapor, a matsayin Ministan Makamashi da Dr Dominic Ahruitinga Ayine a matsayin babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, in ji kamfanin dillancin labaran Ghana.

Kwamitin naɗe-naɗe na majalisar ne ya tantance ministocin uku da aka amince da su ranar Litinin inda ya tantance takardun karatu da ƙwarewa da kuma manufofinsu a ɓangarorin da aka naɗa su.

Bayan kwamitin ya gabatar da sakamakon aikinsa a gaban majalisar, sai ‘yan majalisa suka tafka muhawara game da ƙwarewar ministocin da kuma shirye-shiryensu na warware matsalolin da ƙasar ke fama da su.

Andrew Amoako Asiamah, mataimakin shugaban majalisar da ya jagoranci zaman, shi ya bayyana amincewar majalisar da ministocin a zauren majalisar.

Shugaba John Mahama dai ya kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Ghana ne a wa’adinsa na biyu bayan an rantsar da shi ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2025.

Wannan ne kashi na farko na ministocin da shugaban ƙasar ya miƙa wa majalisar domin tantancewa da amincewa da su.

TRT Afrika