Yaƙin Sudan ya raba sama da mutum miliyan takwas da muhallansu. / Hoto: Getty Images

Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed ta yi maraba da taimakon abincin da ke zuwa Sudan sai dai ta koka kan cewa ba zai isa ba.

Ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai ziyara kan iyakar Sudan din da Chadi a Adre domin tabbatar da wucewar jerin motocin da ke ɗauke da kayan agaji cikin Sudan ɗin.

Amina Mohammed ɗin a yayin ziyarar da ta kai, ta yi kira kan a cim ma matsaya domin kawo ƙarshen wannan yaƙin da aka shafe sama da shekara guda ana gwabzawa.

A lokacin tattaunawar wadda aka yi a Geneva, ɓangarorin biyu masu rikici da juna sun ɗan ƙoƙarta a tattaunanawar inda suka amince su dakatar da yaƙin domin barin kayayyakin agaji su wuce.

Wani ɗan jarida na kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu damar ganin motocin kayan agajin suna shiga yankin na Darfur a lokacin ziyarar da Amina Mohammed ta kai.

Cika alƙawari

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya a wata sanar da ya fitar a ranar Alhamis ya ce manyan motocinsa suna ɗauke da tan 630 na kayan abinci - wanda zai ishi mutum kusan 55,000 — daga Chadi zuwa yankin Darfur.

Amina Mohammed ta ce a lokacin ziyarar da ta kai Adre, wannan "adadi kaɗan ne" na abin da ake buƙata domin rage raɗaɗin da ake ciki a Sudan.

Ta bayyana cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta samu damar taimakawa wurin biyan buƙatun da ake nema da kaso 25 zuwa 30 cikin 100, inda ta ce akwai buƙatar alƙawarin da gwamnati ta yi ta cika shi ta yadda za a taimaka wa mabuƙata.

Fada ya barke a kasar Sudan a cikin watan Afrilun 2023, inda ake gwabazawa tsakanin sojojin kasa karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al Burhan da dakarun RSF ƙarƙashin Mohamed Hamdan Dagalo.

Kungiyoyin agaji sun ce fadan ya hana kai agajin jin kai ga mutanen Sudan miliyan 25 da ke fuskantar matsananciyar yunwa.

TRT Afrika