Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a yi karatu na biyu ga dokar haraji / Hoto: Tope Brown/Nigerian Senate

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya aike wa majalisar da ƙudurin dokar harajin ƙasar wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da ƙudurin a gaban majalisar inda sanatoci suka yi muhawara a kansa.

A ranar 3 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu Bola ya miƙa wa majalisar dokokin ƙasar wasu ƙudurorin gyara dokar haraji guda huɗu domin amincewa da su, sai dai sun jawo ce-ce-ku-ce da suka musamman daga arewacin ƙasar.

Matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce inda gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki suka yi fatali da gyaran dokar harajin.

TRT Afrika