Rundunar 'yansandan jihar Kano ta taimaka wajen hada mai POS din da mutumin da ya yi kuskuren tura masa kudin:Hoto/Rundunar ƴan sandan Kano

Wani mai sana’ar POS a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa yayin da yake son tura masa naira dubu 10, kamar yadda rundanar ƴan sanda reshen jihar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Lamarin ya faru ne a watan Disamba na shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.

Daga nan ne sai mai POS ɗin ya garzaya hedkwatar ƴan sanda da ke jihar Kano ya sanar da su abin da ya faru. Sai ƴan sandan suka ɗauki bayanansa kuma suka buƙaci ya ba su lokaci su gudanar da bincike don gano mutumin da ya tura masa maƙudan kuɗin bisa kuskure.

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ƴan sandan ya fitar ta ce sun kwashe kimanin wata uku suna bincike kafin su gano mutumin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.

Rundunar ƴan sandan ta ce tuni mai POS ɗin ya mayar wa ɗan kasuwar kuɗinsa wato naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in (9,990,000:00). Jin daɗin haka ya sa ɗan kasuwar ya ba mai POS ɗin kyautar naira 500,000. Kazalika rundunar ƴan sandan ta yaba da kyakkyawan halin mai POS ɗin kuma ta buƙaci sauran jama’a da su yi koyi da shi.

A kwanakin baya ma an samu wani ɗan agaji mai suna Salisu Abdulhadi wanda ya tsinci naira miliyan 100 a jihar Katsina kuma ya yi cigiyarsu har sai da aka gano ainihin mai kuɗin, inda aka mayar masa da kuɗinsa.

TRT Afrika