Jami'an tsaro sun bayyana cewa sun gano bindigar gargajiya a gidansa da kuma wasu layu wanda ya yi amfani da su wurin gwajin maganin bindigar da ya haɗa. / Hoto: NPF

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta soma gudanar da bincike bayan wani mai maganin gargajiya ya ɗirka wa kansa harsashi a lokacin da yake gwajin maganin bindiga.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar Joesephine Adeh ta bayyana tun da farko sun samu kira kan cewa wani mai maganin gargajiya mai suna Isma’il Usman ya harbi kansa a daidai lokacin da yake gwajin ƙarfin maganin bindigar da ya haɗa.

Ta bayyana cewa a yayin da yake gwajin sai maganin ya gaza ba shi kariya inda ya ɗirka wa kansa harsashi.

Josephine ta ƙara da cewa tuni aka garzaya da mai maganin gargajiyar asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa kafin daga bisani aka aika shi asibitin ƙwararru da ke Gwagwalada domin samun ƙarin kulawa.

Jami’an tsaron sun bayyana cewa bayan sun gudanar da bincike a gidansa, sun gano wata bindigar gargajiya da layu a gidansu waɗanda ya yi amfani da su wurin gwajin maganin bindigar.

‘Yan sandan sun kuma ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma yunƙurin kashe kansa.

TRT Afrika