Mahamat Idriss Deby ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar Chadi

Mahamat Idriss Deby ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar Chadi

Mahamat Idriss Deby ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya ranar Asabar a N'Djamena, babban birnin ƙasar.
A watannin baya wata kotu a ƙasar Chadi ta bai wa shugaban mulkin soja Mahamat Idriss Deby damar tsayawa takara shugabancin ƙasar/Hoto:Reuters

Shugaban mulkin sojin Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya hau kan mulki bayan mutuwar mahaifinsa a 2021, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi a watan Mayu mai zuwa.

Mahamat Idriss Deby ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya ranar Asabar a N'Djamena, babban birnin ƙasar.

"Ni, Mahamat Idriss Deby Itno, ne ɗan takarar shugaban ƙasa na gamayyar jam'iyyun United Chad coalition a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024," in ji shi.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa.

A tsakiyar watan Janairun da ya gabata, jam'iyyar Patriotic Salvation Movement (MPS) ta ayyana Mahamat Deby Itno a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa.

Deby Itno ya hau kan mulki ne a shekarar 2021 bayan mahaifinsa Idriss Deby Itno, wanda ya kwashe kusan shekara talatin a kan mulki, ya mutu a fagen yaƙi yayin fafatawa da wasu ƴan tawayen ƙasar.

TRT Afrika