Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Masarautun Kano sabbi da ya kirkiro za su ci gaba da zama din-din-din ko da ya bar kan mulki.
Ya bayyana hakan a wurin taron ranar ma’aikata ta duniya wanda aka yi a filin wasa na jihar.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa an yi masarautun ne domin jama’ar jihar Kano kuma ko ba su da gwamnati a hannu za su ci gaba da addu’a.
“Wadannan masarautu an yi su ne domin bada hadin kai, an yi su ne domin ci gaba, an yi su ne domin tarihi, an yi su ne domin daraja sarautar gargajiya,” in ji Gwamna Ganduje.
“Wadannan masarautu an yi su ne domin daraja wadannan al’umma da suke zaune a wadannan wurare kuma ina tabbatar muku wadannan masarautu din-din-din, sun zo da zama da gindinsu,” kamar yadda ya kara da cewa.
“In Allah ya yarda, sai Mahadi ka ture kuma Mahadin da zai ture, Allah ba zai kawo shi ba,” in ji Gwamna Ganduje.
Kalaman na Gwamna Ganduje na zuwa ne bayan kalaman da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya yi game da masarautun Kano inda ya ce akwai bukatar a sake nazari kan kasa masarautun jihar gida biyar.
Kalaman na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce matuka a shafukan sada zumunta.