Ma'aikatan sufurin jiragen sama na zanga-zanga saboda yarjjejeniyar filin jirgin. / Hoto: AFP

Daruruwan ma'aikata a babban filin jiragen sama na kasa da kasa a Kenya sun guanar da zanga-zanga a ranar Laraba don nuna adawa ga yarjejniyar da gwamnatin kasar ta kulla da kamfanin zuba jari na kasar waje.

Fasinjoji da dama ne suka yi cirko-cirko a filin jiragen sama na kasa da kasa na Jomo Kenyatta da ke babban birnin Nairobin Kenya tun ranar Talata, a lokacin da Kungiyar Ma'aikatan Filin Jirgin (KAWU) suka sanar da yjin aikin sai baba ta gani don nun adawa ga shirin gwamnati na mika filin jirgin g kamfnin Adani.

Gwamnatin ta bayyana cewa yarjejeniyar gina-kula da shi-mika wa kasa da aka kulla da AKamfanin Adani za ta bayar da damar yin kwaskwarima ga filin jiragen saman, za a gina sabon titin jirgi, inda shi kuma kamfanin zai kula da filin na tsawon shekaru 30.

Kungiyar Ma'aikatan Filin Jirgin, a sanarwar fara yajin aikin ta ce yarjejeniyar za ta janyo rasa ayyukan yi da kawo 'sharuddan aiki marasa kyau' ga wadnda za su ci gaba da yin aiki.

Gwamnatin ba ta da gaskiya, kuma ba su da aminci. Ba su ba mu dukkan takardun kulla yarjejeniyar ba kamr yadda muk bukta. Abinda muke so kawai shi ne gwamnati ta soke yarjejeniya da kamfanin Adani." in in ji Sakatare Janar na kungiyar ta KAWU Moss Ndiema yayin gana wa da kafafen watsa labarai na kasar a ranar Talata.

Zanga-Zangar ta janyo babban tsaiko, inda matafiya da dama suka makale a kan dogayen layuka inda aka hana tashin jirage, wanda ya sanya aka to hana tashi da saukar jiragen saman cikin gida da na kasashen waje.

Filin jirgin sama na jigilar fasinjoji miliyan 8.8 a shekara amma yana fiuskantar kalubalen rashin kayan aiki, ciki har da zubar ruwa da rufin kwano ke yi, katsewar lantarki da tsufan kayayyaki.

Sabbin yajin aiki

A makon da ya gabata, m'aikatan filin jirgin sun yi barazanar tafiya yajin aiki, amma sai aka dakatar da shirin nasu har sai an gama tattaunawa da bangaren gwamnati.

Ganin yadda wasu mutane da ba a sani ba suna kai komi a filin jirgin, suna daukar hotuna kuma ana yin rubuce-rubuce ya sanya damuwar cewar jami'an kamfanin na India na shirin tabbatar da fara aiki da yarjejeniyar, in ji kafafan yada abarai na cikin gida a makon da ya gabata.

A ranar Liinin Kotun Koli ta dakatar da aik da yarjejeniya zuwa wani dan lokaci, har sai an saurari karar da Kungiyar Lauyoyi da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam na Kenya suka shigar a gabanta.

TRT World