Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Hakan na nufin Aiyedatiwa zai ci gaba da zama a gidan gwamnatin jihar Ondo har zuwa lokacin da za a rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar a karo na biyu bayan ya gaji Rotimi Akeredolu wanda ya rasu a watannin baya.
Aiyedatiwa ya samu ƙuri’u 366,781 a zaɓen jihar inda ya kayar da babban abokin adawarsa Ajayi Agboola na Jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 117,845, kamar yadda hukumar ta INEC ta sanar.
An samu tazarar ƙuri’u 248,936 tsakanin ‘yan takarar wanda hakan ke nufin Aiyedatiwa ya ninka abokin takararsa a yawan ƙuri’u.
Haka kuma sakamakon zaɓen ya nuna jam’iyyar ta APC ta samu nasara a duka ƙananan hukumomi 18 na jihar Ondo.
'Yan takara 18 ne suka fafata a zaɓen na Jihar Ondo wanda aka gudanar a ranar Asabar.
An tsaurara tsaro a jihar a yayin zaɓen inda aka jibge sama da 'yan sanda 22,000 a jihar.