Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a Jamhuriyar Ɗimokuradiyyar Kongo, inda ya ce, "Lokacin zaman lafiya ya yi."
Guterres ya nuna ''matuƙar damuwa'' game da halin da ake ciki, kana ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a hedkwatar MƊD da ke birnin New York cewa ''muna kan wani muhimmiyar gaɓa kuma lokaci ya yi da za mu haɗa kai don samar da zaman lafiya.''
Kazalika Guterres ya bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani taro a Tanzaniya tare da shugabannin ƙungiyar ƙasashen yankin gabashin Afirka da na raya Afirka ta Kudu wanda zai mayar da hankali kan hare-haren 'yan tawayen M23 da kuma artabunsu da sojojin Kongo.
"A mako mai zuwa, zan kasance a Addis Ababa don halartar taron koli na ƙwamitin sulhu da tsaro na Tarayyar Afirka, inda batun wannan rikici zai kasance kan gaba cikin batutuwan da za a fi mayar da hankali a kan su,'' kamar yadda Guterres ya bayyana a ranar Alhamis, yana mai jaddada kiransa na ''samar da zaman lafiya,''
Haka kuma Guterres ya jaddada cewa, barazanar da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Kongo da kuma arangamar 'yan tawayen M23 ya janyo hasarar rayuka masu yawa, inda aka kashe dubban fararen hula tare da tilastawa wasu da dama ƙaurace wa matsuguninsu.
“Halin jinƙai a Goma da kewaye ya yi muni sosai,” in ji shi, yana mai cewa “cibiyoyin kiwon lafiya sun cika maƙil da jama'a.
Babban jami'in na MDD ya bayyana cewa an samu tsaiko na ayyukan makarantu da wutar lantarki da kuma hanyoyin sadarwa, ''rikicin na ci gaba da muni a Kudancin Kivu kana akwai barazanar ya yi mamaye yankin baki ɗaya.''
"A bayyane sakona yake: A ajiye bindigogi, a daina faɗaɗa rikicin sannan a mutunta 'yancin kan ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, tare da kiyaye dokokin kare hakkin bil'adama da kuma jinƙai na ƙasa da ƙasa, babu wata mafita ta hanyar soja," in ji shi.
A kiransa kan shiga tsakani, Guterres ya ce: "Lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan rikici, lokaci na ya yi da za a samar da zaman lafiya. Munin ricikin ya yi yawa."
Rikicin da ya ɓarke a Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa, ya soma ne makonni biyu da suka wuce, lokacin da 'yan tawayen M23 suka ƙaddamar da wani gagarumin farmaki kan dakarun gwamnati.
Hukumar da ke kula da ayyukan jiƙai ta Majalisar dinkin duniya OCHA, ta ce an kashe mutane fiye da 2,900, yayin da kusan 3,000 suka jikkata.
Dubban mutane sun rasa matsugunansu, kana da dama sun tsere zuwa maƙwabciyar ƙasar Rwanda, ciki har da ma'aikatan ƙungiyoyin kasa da kasa kamar na MDD da Bankin Duniya.
A ranar Litinin ne 'yan tawayen M23 suka fitar da snaarwar tsagaita wuta bayan fafatawar kwace birnin Goma da sojojin Kongo