Kasar Libya ta mayar da baƙin haure 369 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba a ranar Talata zuwa ƙasashensu Nijeriya da Mali, da suka haɗa da mata da yara sama da 100, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mohammed Baredaa, shugaban kungiyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Libya da aka ɗora wa alhakin dakatar da yin hijira ba bisa ƙa’ida ba, ya ce an yi sawu biyu na jigilar ‘yan Nijeriya 204 da kuma ‘yan kasar Mali 165 don mayar da su gida.
Baredaa ya ce jarirai tara da yara ƙanana 18, da mata 108 na daga cikin ‘yan ci-ranin Nijeriya da aka mayar gida.
Ya ce an gudanar da jigilar ne "da hadin gwiwar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM)".
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya tana mayar da 'yan ci-ranin ƙasashensu kyauta tare da taimaka wa sake shigar da su cikin kasashen nasu ta hanyar "shirin dawowar jinƙai na sa kai".
Sai dai wasu baƙin hauren sun shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP a ranar Talatar da ta gabata cewa ana tirsasa su komawa gida.
Hukumomin Libya sun zo da dare suka karya ƙofa, in ji Hakim mai shekaru 59, dan Nijeriya da ya yi rayuwa a Libya tsawon shekaru 25 wanda ya ƙi bayyana sunansa.
He said they confiscated his passport before detaining him and his wife prior to repatriation.
Ya ce sun kwace fasfo din sa kafin su tsare shi da matarsa kafin a dawo da su gida.
Har yanzu Libya na fafutukar farfaɗowa daga shekaru da dama da aka kwashe ana yaƙi da hargitsi bayan hambarar da gwamnatin Moamer Ghaddafi da NATO ta yi a shekara ta 2011.
Masu fasa-kwauri da masu safarar mutane sun yi amfani da yanayin rashin zaman lafiya da ya mamaye fadin kasar tun daga lokacin.
Ana sukar kasar Libya kan yadda take tafiyar da baƙin haure da 'yan gudun hijira, tare da zargin kungiyoyin kare hakkin bil'adama da suka hada da karbar kudi zuwa bauta.
Kasar wadda take da tazarar kilomita 300 (mil 186) daga Italiya, ta zama muhimmiyar wurin tashi ga baƙin haure, musamman daga kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, da ke fuskantar hatsarin balaguro ta Tekun Bahar Rum don neman ingantacciyar rayuwa a Turai.
Sai dai a kokarin da Libya da Tarayyar Turai ke yi na daƙile kwararar baƙin haure ba bisa ƙa'ida ba, da dama sun tsinci kansu a maƙale a Libya.
A farkon wannan watan, hukumomin Libiya sun ce kusan baƙi huɗu cikin biyar daga cikin 'yan kasashen waje da ke kasar da ke arewacin Afirka ba su da takardun shaida.
"Lokaci ya yi da za a warware wannan matsala", in ji Ministan Harkokin Cikin Gida Imad Trabelsi a wancan lokacin, ya ƙara da cewa Libya ta juya daga "kasar da ake yada zango zuwa matsuguni na dindindin" - abin da yake ganin "ba za a amince da shi ba".