Baƙin hauren da ke neman tsallakawa tekun mai hatsarin gaske zuwa Turai daga arewacin Afirka sukan faɗa hannun ƙungiyoyin fataucin da ke karɓar kudi.

A ranar Talata ne Libya ta mayar da 'yan ci-rani kusan 1,000 ƴan ƙasashen Masar da Nijeriya gida, wadanda suka yi zamansu a ƙasar ta arewacin Afirka ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda jami'ai da 'yan jaridar AFP suka bayyana.

An mayar da Misarawan 664 ta motar bas zuwa kan iyakar Emsaed da Masar, kusan kilomita 1,400 gabas da Tripoli.

Janar Mohamad Bardaa, wanda ke jagorantar hukumar hana shige da fice ta kasar mai alaƙa da ma'aikatar harkokin cikin gida, ya ce an kai 'yan Nijeriya 300 filin jirgin sama domin mayar da su gida.

Libya, ta faɗa cikin ruɗani tun bayan hamɓarar da gwamnatin Moamer Ghaddafi a shekara ta 2011, kuma a yanzu tana karkashin kulawar gwamnatoci masu adawa da juna a yammaci da gabashin ƙasar, kuma ta zama cibiyar yin hijira ba bisa ƙa'ida ba zuwa Turai.

Baƙin hauren da ke neman tsallakawa tekun mai hatsarin gaske zuwa Turai daga arewacin Afirka sukan faɗa hannun ƙungiyoyin fataucin da ke karɓar kudi.

Dubban mutane, akasari 'yan ƙasar Masar ne suka shafe shekaru da dama suna zaune ba bisa ƙa'ida ba a ciki da wajen babban birnin ƙasar ta Libiya, suna aikin noma da kasuwanci da aikin gine-gine.

A irin wannan aiki a watan da ya gabata, an mayar da Misarawa 600 gida a ranar 6 ga watan Nuwamba, sannan aka mayar da 250 Nijar da Chadi a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Alƙaluman Hukumar Kula da masu Ƙaura ta Duniya sun nuna cewa akwai yan ci-rani fiye da 700,000 - mafi yawansu daga Nijar da Masar da Libiya daga tsakanin watan Mayu zuwa Yunin bana.

AFP